Allah Ya Baka Lafiya: Dino Melaye Ya Yi Ba’a Ga Tinubu Kan Subul da Baka da Yayi a Wajen Kamfen
- Kwamitin kamfen din Atiku Abubakar ya yi ba'a ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC kan barambaraman da yayi a jihar Lagas
- Bola Tinubu ya yi subul da baka a wajen kamfen dinsa inda ya kira PVC da APV-APC
- Da yake martani, Dino Melaye ya yi addu'an Allah ya baiwa Tinubu lafiya yana mai cewa masu tura shi yayi takara basa kaunarsa
Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye, ya zolayi Asiwaju Bola Tinubu, kan subul da baka da yayi a yayin gangamin yakin neman zabensa a jihar Lagas.
Yayin da yake jawabi ga dumbin magoya baya a mahaifarsa a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba, dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya bukace su da su je su karbi katin ‘APV’.
Koda dai alamu sun nuna yana nufin katin zabe (PVC), tsohon gwamnan na jihar Lagas ya gyara zancensa ta hanyar cewa APC.
Tinubu ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Shin kuna so na? Kuna so na? Ku je ku karbi APV…APC kuma dole ku zabe ni.”
Karara ya nuna cutar mantuwa na damun Tinubu, Dino
Da yake martani, Melaye ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:
“Me yasa mutanen nan ke yiwa mutumin nan mgunta? Ya kira PVC, APV sannan ya gyara kansa ta hanyar kiransa APC. Cutar mantuwa ne wannan faa. Allah ya baka lafiya Tinubu. SDM.”
Kalli wallafar tasa a kasa:
Jama’a sun yi martani
Ifechukwu Fenop Anujulu ya ce:
“Ko da APV ko APC duk da haka ya yi kuskure, wannan abun ba zai taba faruwa ga Najeriya ba. Duk zamu dauki PVC dunmu sannan mu yi waje da su.”
Basil Ohazulike ya ce:
“Wadanda ke tura mutumin nan don ya zama shugaban kasar Najeriya basa kaunarsa. Aikin zai yi masa yawa kuma zai iya takaita rayuwarsa.”
Anabuike Emeka ya ce:
“Su je su karbi APV dinsu…Mu kuma zamu yi amfani da PVC dinmu wajen daidaita Najeriya ta hanyar PO.
Dapo Ojuade Balogun ya yi martani:
“Tinubu ya rigada ya zama babban kwamanda a 2023. Ka san da haka ka samu nutsuwa.”
Kulekule Thaddeus Igbawua ya ce:
“A kyalesa shi kadai. Tinubu ba zai iya komawa gidansa bayan zuwa unguwa ba saboda yawan mantuwa…hakan na nufin abubuwa da yawa.”
Asali: Legit.ng