Tinubu Ya Sake Baranbarama, Ya Kira Katin Zabe PVC da APV-APC

Tinubu Ya Sake Baranbarama, Ya Kira Katin Zabe PVC da APV-APC

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sake tafka kuskure yayin jawabi ga jama'a lokacin kamfe
  • Karo na uku kenan cikin yan makonnin nan da zai tafka irin wannan kuskuren
  • Wasu yan Najeriya na ganin cewa dan takaran kujerar shugaban kasan bai isasshen lafiya

Legas - Dan takara a zaben neman kujerar shugaban kasar Najeriya karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ya sake baranbarama a wajen kamfe.

Jirgin yakin neman zaben Jam'iyyar ta APC ta yada zango mahaifarsa ta Legas a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba, 2022.

Tinubu
Tinubu Ya Sake Baranbarama, Ya Kira Katin Zabe PVC da APV-APC
Asali: Twitter

Yayin jawabi da gangamin mabiya dake wajen taro a filin kwallon Teslim Balogun, tsohon gwamnan na Legas yace su je su karbi katin "APV".

Yayinda yake kokarin gyarawa kuma ya sake tafka wata baranbaramar yace APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace:

"Shin kuna so na? Ku je ku karbi APV...APC kuma wajibi ne kuyi zabe,"

Kalli bidiyon:

Ba yau farau ba

Dan takaran na APC ya kwan biyu yana subut-da-baka yayin jawabi ga jama'a a kwanakin nan.

A lokacin taron kamfen farko da APC ta gudanar da garin Jos, jihar Plateau, Tinubu ya yiwa jam'iyyar PDP addu'a maimakon APC.

A jihar Kaduna kuwa yayin kokarin jinjinawa El-Rufa'i, ya sokesa.

Yace:

"El-Rufa'i ya mayar da rubabben lamari lalatacce."

Shi yasa wasu suka yi kin halartan taron muhawarar ARISE Tv da Tinubu yayi, yana tsoron magana ne saboda bai da isasshen lafiya.

A jawabin da mai magana da yawun kamfensa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce Tinubu ba zai halarci taron muhawarar ba.

Yan Najeriya da dama na zargin cewa Tinubu bai da isasshen lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel