Atiku: Zan Fitar Da Sunayen Ɓarayin Man Fetur, Zan Kunyata Su Idan An Zabe Ni Shugaban Ƙasa A 2023
- Masu satar danyen man fetur a Najeriya za su shiga uku idan har Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar PDP ya ci zabe a shekarar 2023
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa idan ya ci zabe, zai tattara sunan masu satar mai, ya fitar da sunayen su kuma ya bincike su
- Atiku ya kuma ce zai kwace rijiyoyin man fetur daga hannun duk wadanda aka basu amma ba su habbaka su ba ya bawa wadanda za su habbaka su
Jihar Legas - Barayin man fetur da masu hada baki da su ba za su cigaba da samun mafaka ba duk girmansu a kasa idan jam'iyyar PDP ta karbi mulki a shekarar 2023, rahoton Daily Trust.
Wannan shine alkawarin da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya yi, lokacin da ya tattauna da jagororin kamfanonin yan kasuwa a Eko Hotel da ke jihar Legas a ranar Asabar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wasu shugabannin kamfanoni a wurin taron sun hada da Alhaji Aliko Dangote, Jim Ovia, Femi Otedola, Tony Elumelu, Herbert Wigwe, Muhammad Hayatudeen da sauransu.
Zan kwace rijiyoyin mai na wadanda ba su aiki da shi - Atiku
Atiku, ya kuma ce saboda cigaban kasa zai kwace rijiyoyin man fetur daga hannun wasu yan Najeriya da ba su aiki da su, The Punch ta rahoto.
Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya yi alkawarin zai cigaba da tattaunawa da gwamnati da yan kasuwa idan an zabe shi, kuma zai bayyana hanyoyin farfado abin da ya kira tattalin arzikin da ya kira 'mara lafiya'.
Atiku ya fada wa masu ruwa da tsakin cewa:
"Idan ba za ku habbaka rijiyoyin man fetur ba, za mu kwace mu bawa wadanda za su habbaka shi. Za mu tattara sunayen wadanda ke satar mai, za mu wallafa sunayen kuma mu bincike su."
PDP a Jihar Filato ta yi wa Atiku Abubakar alkawarin kuri'u miliyan 2 a zaben 2023
A bangare guda, jam'iyyar PDP reshen jihar Filato ta yi wa dan takararta na shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar alkawarin kuri'u guda miliyan biyu a zaben shekarar 2023.
AIT ta rahoto cewa jiga-jigan jam'iyyar a jihar sun sanar da hakan ne yayin gangamin kaddamar da kwamitin kamfe din Atiku-Mutfwang a Jos, babban birnin jihar ta Filato.
Asali: Legit.ng