Yanzu Yanzu: Kiristocin APC a Arewa Sun Tsayar Da Peter Obi Don Ya Gaje Buhari a 2023
- An bukaci kiristocin jihohin arewa 19 su yi watsi da Bola Tinubu da Kashim Shettima na APC
- Wata kungiyar fusatattun kiristocin APC daga arewa karkashin jagorancin Babachur Lawal ne suka yi kiran
- A cewar kungiyar, Tikitin Musulmi da Musulmi na APC shaidanci ne kuma dole daukacin kiristocin arewa suyi watsi da shi
Kungiyar fusatattun kiristocin APC na arewa sun yi watsi da takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima.
Kungiyar ta ba mambobinta da magoya bayanta shawarar goyon bayan tikitin Obi/Datti a zaben 2023, New Telegraph ta rahoto.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken "dalilin da yasa muka zabi goyon bayan tikitin Obi/Datti" dauke da sa hannun daya daga cikin shugabanninta, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal.
Peter Obi da Datti Baba-Ahmed za mu yi
Shugaban Kasa a 2023: Jerin Manyan Jiga-jigan APC 6 Da Basa Goyon Bayan Tinubu Saboda Tikitin Musulmi da Musulmi
A cewar Lawal, kungiyar ta yanke shawarar marawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Parth, Peter Obi da abokin takararsa, Yusuf Datti Baba-Ahmed baya bayan sun yi nazari da auna sauran tikitin takarar, rahoton Channels TV.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake ci gaba da bayani, Lawal ya bayyana tikitkin Musulmi da Musulmi na APC a matsayin shaidanci.
Kungiyar ta kara da cewar da gangan aka kitsa haka da kuma shirin haddasa sabanin addini a tsakanin yan Najeriya, yana mai cewa yan arewa ne mutanen da suke hari.
Ya bayar da shawarar kin zaban dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu da abokin takararsa Kashim Shettima.
Kungiyar ta ce ta yarda da cewar tikitin Obi/Datti zai ba Najeriya sararin shakar iska mai ni'ima da damar kwato kasar daga halin da wasu masu son rai suka jefa ta.
Ko a jikinmu: APC ta yiwa Babachir addu'an Allah kiyaye hanya a yunkurinsa na goyon bayan Atiku Abubakar
A wani labarin, APC ta nuna ko a jikinta barazanar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal yayi inda ta ce ko kadan rashinsa a tawagar magoya bayan Bola Tinubu ba zai hana shi cin zabe ba.
Jam'iyyar mai mulki ta ce ko a da chan babu abun da Babachir ya tsinana domin dai bai kawo mazabarsa ba a zabukan 2015 da 2019.
Asali: Legit.ng