Ko Da Tsiya-Tsiya Sai Mun Lashe Zabe A Kano: Shugaban APC, Abdullahi Abbas

Ko Da Tsiya-Tsiya Sai Mun Lashe Zabe A Kano: Shugaban APC, Abdullahi Abbas

  • Jam'iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zaben gwamnan jihar Kano da za'a yi a Maris 2023
  • Shugaban jam'yyar ta jihar ya sake maimaita abinda ya fadi a 2019 cewa ko ta kaka zasu lashe zaben
  • Mataimakin gwamnan jihar, Yusuf Gawuna, ne dan takara yayinda Sule Garo zai yi masa mataimaki

Kano - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, a ranar Laraba ya bayyana cewa ko da tsiya-tsiya sai sun lashe zaben gwamnan jihar a 2023.

Abbas ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin taro kaddamar da yakin neman zaben jihar a masarautar Gaya, rahoton Punch.

Ya bayyana dimbin magoya bayan APC cewa jam'iyyar APC ke da mulki a jihar kuma kada wani yayi tunanin zasu zuba ido wani ya kwace mulki daga hannunsu a bagas.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu Ya Gamu Da Koma Baya A Yayin Da Manyan Yan APC 400 Suka Koma Bangaren Atiku

Abdullahi Abbas
Ko Da Tsiya-Tsiya Sai Mun Lashe Zabe A Kano: Shugaban APC, Hoto: Abdullahi Abbas
Asali: Twitter

Yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mutane na cewa in daina fadin APC zata kwace Kano ko da tsiya-tsiya. Ina son fadin muku cewa APC za ta mamaye Kano ko da tsiya-tsiya. Mun shirya tsaf don lashe kuri'un daga sama har kasa a 2023."
"Kamar yadda kuka sani Gaya gidan APC ce; babu wata jam'iyyar da tafi karfinmu da fada a aji. Shirye muke da muyi duk mai yiwuwa don cigaba da mamayeta. Gawuna dan takaranmu ne kuma shi zai zama sabon gwamnan jihar Kano."

Shi kuwa dan takaran gwamnan jihar na APC, wanda shine mataimakin gwamna yanzu, Dr Nasiru Yusif Gawuna, ya bayyana cewa shirye yake da ya tunkari zaben saboda yana da goyon bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da jiga-jigan jam'iyyar, riwayar Thisday.

A cewarsa:

"Na yi imani kaddara ta na hannun Allah kuma babu shakka da yardan Allah babu abinda zai hana ni nasara a zaben nan. Jam'iyyarmu za tayi tsayin daka."

Kara karanta wannan

A ci gaba kawai: APC ta ce tana jin dadin rikicin cikin gida na PDP a wata jihar Arewa

Ya jinjinawa magoya bayansu da suka halarci taron.

Damfarar $1.3m: Kotu ta umarci EFCC ta kamo wani dan takarar sanatan APC a Kano

Jam'iyyar APC na cikin rikici sakamakon bacewar dan takaran kujerar Sanata mai wakiltar birni, AA Zaura.

Kotun tarayya mai zama a jihar Kano ta umarci hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC da ta sankamoshi duk inda yake.

Asali: Legit.ng

Online view pixel