2023: Tinubu Ba Zai Ba ’Yan Najeriya Kunya Ba, Dan Majalisa
- Mamban majalisar wakilai ta kasa mai wakiltar Ondo ta Gabas ya magantu kan yadda Tinubu zai yi mulkinsa bayan 2023
- Ya ce sam dan takarar shugaban kasan na APC ba zai ba 'yan Najeriya kunya ba matukar aka zabe shi a zaben 2023
- Ya kuma bayyana cewa, Tinubu ya kafa tarihi a Legas, kuma zai yi irin hakan idan aka zabe shi ya gaji Buhari
Jigar Ondo - Mamban majalisar wakilai ta kasa daga Ondo ta Gabas, Abiola Makinde ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ba zai ba 'yan kasar nan kunya ba.
Ya bayyana cewa, matukar 'yan Najeriya suka Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023, to tabbas kakarsu ta yanke saka, Punch ta ruwaito.
Makinde ya bayyana wannar magana ta goyon baya ne a wani taron gangamin tallata APC da Tinubu da aka gudanar.
Masoya Tinubu sun yi tattaki tsakanin kananan hukumomi biyu na Ondo ta Gabas da ta Yamma don nuna kaunarsu ga dan takarar na APC.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ku zabi Tinubu, Makinde ya fadi dalilai
A jawabin, Makinde ya bukaci 'yan Najeriya da suk zabi Tinubu a 2023 da ma sauran 'yan jam'iyyar domin ganin ci gaba bayan zaben 2023.
A kalamansa:
"Mun zo ne don yabawa jama'a bisa nuna goyon bayansu ya zuwa yanzu kuma muna tabbatar muku cewa ba za mu baku kunya ba idan kuka zabi dan takararmu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu a zaben Fabrairun badi. Asiwaju ba zai ba 'yan Najeriya kunya ba idan aka zabe shi.
"Kun san ni a matsayin danku, kuma ba zan yi fiye da abin da nayi a wa'adina na farko ba da baku zabe ni na wakilce ku a majalisar kasa ba.
"Ina kira gareku da ku zabi dukkan 'yan takarar jam'iyyarmu, APC, a babban zaben 2023 daga kan shugaban kasa har mamban majalisar dokoki na jiha."
A nasa jawabin, dan takarar sanata na Ondo ta tsakiya, Mr Niyi Adegbomire shi ma ya bukaci jama'a da su ba da kuri'unsu ga Tinubu a zaben 2023.
Ya kuma bayyana cewa, Tinubu na da tarihi mai kyau na aiki tukuru a jihar Legas yayin da ya yi gwamna tsawon shekaru takwas.
A jiya ne Tinubu yace tabbas akwai yiwuwar Buhari ya jefa Najeriya cikin yunwa, amma ya tabbatar da daura kasar nan a kan turba.
Asali: Legit.ng