Na Hannun Daman Atiku Ya Maida Martani Ga Kwankwaso Kan Kalaman Faduwar PDP

Na Hannun Daman Atiku Ya Maida Martani Ga Kwankwaso Kan Kalaman Faduwar PDP

  • Kalaman da ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya yi kan Atiku sun bar baya da ƙura
  • Tsohon ministan Sufurin jiragen sama, Osita Chidoka, ya taƙali tsohon gwamnan Kano, yace ya lissafinsa ba haka yake ba
  • Mista Chidoka, makusancin Atiku Abubakar, yace ba'a taɓa samun jam'iyyar da ta lashe jihohi ukun da Kwankwaso ke magana ba

Lagos - Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka, a jiya Talata ya maida martani ga ɗan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.

Jaridar Vanguard tace Chidoka ya tanka wa Kwankwaso ne kan kalaman da ya yi cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ba zai kai labari ba idan har jihohin Legas, Kano da Ribas suka kucce masa.

Kwankwaso da Atiku.
Na Hannun Daman Atiku Ya Maida Martani Ga Kwankwaso Kan Kalaman Faduwar PDP Hoto: Rabiu Kwankwaso, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Idan baku manta ba tsohon gwamnan jihar Kano, Kwankwaso, ya yi wannan hasashen ne yayin kaddamar da wani aiki da gwamna Nyesom Wike ya kammala a jihar Ribas ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Wike Zai Koma Bayan Tinubu? Gaskiya Ta Fito Yayin da Gwamnan APC Ya Faɗi Wata Bukata

Da yake hira da Channels tv cikin shirin Sunrise Daily, Chidoka, makusancin Atiku kuma jigo a PDP, ya ayyana hasashen Kwankwaso da, "Kwacewar lissafi."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin nuna amincewarsa da cewa jihohin ukun zakuna ne masu tulin kuri'u, Mista Chidoka yace ba'a taɓa samun jam'iyyar da ta lashe baki ɗaya jihohin ba a tarihin jamhuriya ta huɗu a Najeriya.

A kalamansa, tsohon ministan yace:

"Jam'iyyar da ta samu nasara a kowace shiyya ce ke cin zabe a Najeriya, ba'a taba samun jam'iyyar da ta lashe jihohin uku a lokaci ɗaya ba, mafi yawa biyu ake ci kamar a 2019, APC ta lashe Kano da Legas, PDP ta ci Ribas."

Akwai wasu jihohin saɓanin waɗannan masu kuri'u - Chidoka

Chidoka, wanda ya bayyana cewa jam'iyyarsa PDP ta lashe zaɓen shugaban ƙasa aƙalla sau uku tun 1999, duk da bata samun nasara a Kano, yace:

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Ya Tsoma Baki a Rigimar Atiku da Gwamna Wike, Ya Faɗi Wanda Ke Kan Gaskiya

"Kamar yadda ake batun Kano to akwai Katsina, haka Legas akwai Delta, ga Jigawa da Akwa Ibom waɗanda basu da yawan kuri'u amma masu kaɗa kuri'a na fitowa sosai idan aka duba tarihi."
"Kano na da kuri'u sama da Miliyan 1.8m, sama da kowance jiha a zaɓen 2019, yayin da Legas ke da kuri'u sama da miliyan ɗaya da Ribas mai kuri'u dubu 600,000 a wancen zaɓen. Kano da Legas na hannun APC, Ribas na wurin PDP."

Tsohon Sarkin Kano, Khalifa Sanusi II Ya Bayyana Ɗan Takarar Da Yake Goyon Baya a 2023

A wani labarin kuma Sarkin Kano na 15, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya umarci 'yan Tijjaniyya a Kaduna su mara wa ɗan takarar APC baya a zaɓen 2023

A wurin wani taron shekara-shekara da wata ƙungiyar Tijjaniyya ta shirya a Kaduna, Sheikh Tijjani Auwal, yace Khalifa ya faɗa musu ɗalilin goyon bayan Uba Sani.

Haka nan kuma Shehin Malamin ya bayyana cewa jagoran Tijjaniyya a Najeriya ya faɗa musu wanda zasu zaɓa ya zama gwamnan jihar Kano a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262