Kaduna: Khalifa Muhammad Sunusi II Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Ɗan Takarar APC a 2023

Kaduna: Khalifa Muhammad Sunusi II Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Ɗan Takarar APC a 2023

  • Khalifan Tijjaniyya a Najeriya ya umarci mabiya Ɗarika su zabi Sanata Uba Sani a matsayin gwamnan jihar Kaduna a 2023
  • A wurin wani taron shekara-shekara na ƙungiyar Tijjaniyya, Khalifa ya faɗi matsayarsa duk da ba ya cikin kowace jam'iyya
  • Malam Uba Sani ya nuna jin daɗinsa bisa samun wannan gagarumin goyon baya daga Khalifa Sanusi II

Kaduna - Tsohon Sarkin Kano kuma jagoran Ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya, Khalipha Muhammad Sanusi II, ya nuna goyon bayansa ga ɗan takarar gwamnan Kaduna a inuwar jam'iyyar APC.

Sheikh Tijjani Sani Auwal Inyass, ɗaya daga cikin masu faɗa aji a Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya ne ya bayyana haka a taron shekara na farko na ƙungiyar Tijanniya Grassroots Mobilisation and Empowerment (TIGMIEN).

Khalifa Muhammad Sanusi II.
Kaduna: Khalifa Muhammad Sunusi II Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Ɗan Takarar APC a 2023 Hoto: Leadership
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Daraktan sadarwa na kwamitin kamfen APC a Kaduna, Mallam Ibrahim Musa, ya fitar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Ramuwar Gayya Muka Yi': Kotu Ta Yanke Wa Wasu Makiyaya Uku Hukunci Kan Ƙone Gonar Gyaɗa Ta Miliyan N1.5m

Sanarwan ta haƙaito Sheikh Tijjani Auwal na cewa Khalifa Sanusi ya faɗa musu cewa ba shi da alaƙa da kowace jam'iyyar siyasa a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, Sarkin Kano na 14 ya umarci kafatanin mabiyan Ɗariƙa a Kaduna su zaɓi Sanata Uba Sani a zaɓen gwamnan jihar Kaduna da ke tafe a shekarar 2023.

Meyasa Khalifa Sanusi Ya umarci a zaɓi Uba Sani?

Daraktan Sadarwa na kamfen Uba Sani ya ƙara da cewa Sarkin Kano na 14 ya faɗi muhimmin dalilinsa na baiwa Sheikh Tijjani umarnin mabiya su zaɓi APC a Kaduna.

Tijjani yace:

"Khalifa Sanusi da Gwamna El-Rufai abokaine tun na yarinta kuma sun rike junansu da daɗi ko ba daɗi. Saboda haka ba abinda zai hana Khalifa goyon bayan ɗan takarar Malam El-Rufai."

Bugu da Ƙari, Sheikh yace tsohon Sarkin ya faɗa musu wanda zasu zaɓa a zaɓen gwamnan Kano amma ba zai faɗa ba har sai ranar da ya kai ziyara birnin Dabo.

Kara karanta wannan

Komai Ya Yi Farko: Gwamnan Arewa Ya Zubar Da Hawaye Yayin Gabatar da Kasafin Kudi Na Karshe

Na yi farin ciki da matakin Khalifa - Uba Sani

Da yake jawabi a wurin taron, Uba Sani ya gode wa ƙungiyar TIGMEIN bisa gayyatar da suka masa, inda ya ƙara da cewa ya ji daɗin goyon bayan da ya samu daga Khalifa, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Sanatan ya yi alƙawarin kafa kwamitin da zai duba tare da tallafa wa marayu. Ya kuma shawarci masu kaɗa kuri'u su bincike hali da tarihin kowane ɗan takara kafin su zaɓe shi.

A wani labarin kuma Gwamna Masari Ya Zubda hawaye lokacin da yake gabatar da Kasafin kuɗi na ƙarshe a matsayin gwamnan Katsina

Masari, tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya ya gabatar da Kasafin 2023 ga majalisar dokokin jihar Katsina ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba, 2022.

Bayanai sun nuna cewa gwamnan ya gaza rike hawayensa har suka zubo ne yayin da yake bayanin a ƙiyasi Kasafin 2023 bai kai yawan na baɗa 2022 ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaban Jami'ar Wata Jiha a Arewa, Farfesa Muhammad Ya Rasu

Asali: Legit.ng

Online view pixel