Gwamna Ya Tsinci Kansa A Matsala Kan Sukar Peter Obi, Matasan Ibo Sun Bayyana Matakin Da Za Su Ɗauka A Kansa

Gwamna Ya Tsinci Kansa A Matsala Kan Sukar Peter Obi, Matasan Ibo Sun Bayyana Matakin Da Za Su Ɗauka A Kansa

  • Matasan Ibo da ke goyon bayan takarar Peter Obi ba su ji dadin kalaman da gwamnan jihar Anambra ya yi kan dan takarar na LP ba
  • Hakan ne zuwa ne a yayin da matasan suka yi wa Gwamna Chukwuma Soludo barazanar cika gidan gwamnati ta shara idan bai janye kalamansa ba
  • Amma, sun sake bawa gwamnan sabuwar sharadi a yayin da suka nuna bacin ransu game da kalamansa

Matasan Ibo, karkashin kungiyar shugabannin matasa na kudu maso gabas (COESYL) sun yi barazanar cika gidan gwamnatin jihar Anambra da shara kan kalaman da gwamna Chukwuma Soludo ya yi kan dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi.

COSEYL, wacce ta nuna bacin ranta kan Soludo saboda kalaman rashin-goyon bayan Obi, sun bawa gwamnan zuwa ranar Juma'a, 25 ga watan Nuwamba ya janye kalamansa ko kuma ya fuskanci fushin matasan Ibo, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ka gwada idan ba ga tsoro ba: Ganduje ya tsokano Kwankwaso, ya ce Tinubu ya fi shi sanuwa a Kano

Peter Obi da Soludo
Gwamna Ya Tsinci Kansa A Matsala Kan Sukar Soludo TV
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan Ibo sun yi wa Soludo barazana

A sanarwarsa da shugaban kungiyar, Goodluck Ibem, ya fitar ta ce lokacin ya yi da duk wani dan siyasan Ibo mara kishin yankinsa zai dandana kudarsa, jaridar The Sun ta kara.

Ibem ya ce:

"Mun tsayar da ranar Juma'a 25 ga watan Nuwamban 2022 a matsayin ranar da za su debi shara, da bola mu zaba a kofar gidan gwamnatin jihar Anambra don zama izina ga yan siyasar Ibo masu rike da mukami wadanda ke son cin mutuncin kasar Ibo.
"Zubar da shara a gaban gidan duk wanda ya aikata abin Allah-wadai ga al'ummarsa shine hanyar hukunta shi a gargajiyance a kasar Ibo."

Zaben 2023: Wike ya yi wa Soludo izgili, ya bayyana yan siyasa wadanda ba su goyon bayan Peter Obi a kudu maso gabas

Kara karanta wannan

Yan Bijilanti Sun Kashe Mayakan Boko Haram 3, Sun Kwato Makamai Da babur

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba, ya bukaci dan takarar shugaban kasa na Labour Party, LP, Peter Obi, ya dena kula masu masa hassada, musamman yan jiharsa ta Anambra.

Gwamnan na jihar Ribas ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da gadan sama na Nkpolu-Oroworokwo da ke Fatakwal, babban birnin jihar.

Obi bako na musamman ne yayin kaddamar da gadar da mutane da dama suka halarta suna ambaton sunan dan takarar na LP yayin da ya hau mimbari zai yi jawabi.

2023: Peter Obi Babbar Barazana Ce Ga Nasarar PDP, Gwamnan Anambra

Gwamnan jihar Anambra, Chukuwma Soludo, ya ayyana cikakken goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APGA, Farfesa Peter Umeadi.

Gwamna Soludo ya ce ɗan takarar Labour Party (LP), Peter Obi, da magoya bayansa da suka shahara da 'Obidients' ba wata barazana bace ga jam'iyyar APGA, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164