Fitaccen Malamin Addini Ya Umarci Mutane Da Kar Su Zabi Jam'iyyar APC a Zaben 2023
- Har yanzu shawarar jam’iyyar All Progressive Congress (APC) na yin tikitin Musulmi da Musulmi na shan suka
- Babban limamin Katolika na Kaduna, Rabaran Mathew Ndagoso ya ce dole duk jam’iyyar siyasa da ke da irin wannan tunanin ta fuskanci hukunci
- Ya fadama kiristoci cewa kada a zabi jam’iyyar da bata karfafa ka’idar adalci, hadin kai da daidaito
Kaduna – Babban limamin Katolika na Kaduna, Rabaran Mathew Ndagoso, ya bukaci Kiristoci da kar su zabi jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki a babban zabe mai zuwa saboda tsayar da yan takara Musulmi da Musulmi.
Kamar yadda Channels TV ta rahoto, malamin ya ce hukuncin tsayar da mabiya addini daya ya saba ka’idar adalci, hadin kai da daidaito a kasa mai yalwa irin Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 21 ga wayan Nuwamba a Kaduna yayin da yake jaddada cewar addini na taka muhimmiyar rawar gani a bangaren siyasa kuma dole kowace jam’iyyar siyasa ko dan siyasar Najeriya yayi aiki da hakan.
Ya ci gaba da bayyana cewa duk jam’iyyar siyasa da bata damu da muhimmancin addini a yanayin zamantakewa da siyasa ba zata gamu da illar jahiltan lamarin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rabaran Ndagoso ya bayyana cewa kada wani Kirista da ya fita zabe sannan ya jefa kuri’a ga jam’iyyar da bata damu da kasar ba face kansu.
Rabaran Ndagoso ya yi kira ga tsayrara tsaro don zaben 2023
Da yake zantawa da manema labarai, malamin ya kuma magantu kan yanayin tsaro a wasu yankunan kasar.
Ya bayyana cewa yanayin rashin tsaro a kasar nan na nuna babban barazana ga zaben 2023.
Rabaran Ndagoso ya bukaci hukumomin tsaro da fadar shugaban kasa da su dauki matakan kariya da tsaro ga masu zabe da kayayyaki a fadin kasar, rahoton Daily Post.
Tinubu na da kyakkyawar alaka da kiristoci, Jigon APC
Mun kawo a baya cewa babban jigon jam'iyyar APC daga yankin kudu maso gabas, Achom Ihim, ya yi kira ga Kiristocin Najeriya da su sanya ransu a inuwa domin dai Bola Tinubu baya kinsu.
A cewar Ihim, akwai kyakkyawar alaka tsakanin kiristoci da dan takarar shugaban kasar na jam'iyya mai mulki wanda ahlinsa kadai sun isa shaida don duk kiristoci ne su.
Asali: Legit.ng