Kwankwaso Ya Tsoma Baki a Rikicin Wike da Atiku, Ya Fadi Wanda Ke Kan Gaskiya
- Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Kwankwaso yace tsagin Wike G5 na tafiya kan gaskiya game da rikici PDP
- Kwankwaso, yayin kaddamar da ayyuka a Ribas, yace ya ji daɗin yadda tawagar G5 ke tafiyar da harkokinsu kan tafarkin da ya dace
- Tsohon gwamnan ya bayyana dalilin da yasa ya raba gari da manyan jam'iyyun ƙasar nan PDP da APC
Rivers - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace 'Tawagar gaskiya' da ya haɗa wasu gwamnonin PDP suna tafiya kan tafarkin gaskiya game rikicin jam'iyyar.
Da yake jawabi a wurin kaddamar da Hanyoyin Mgbutanwo a jihar Ribas ranar Litinin, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP, Kwankwaso, yace gwamnonin karkashin Wike su ne a kan gaskiya.
The Cable ta rahoto Kwankwaso na cewa:
"Na yi imani su mutane ne masu gaskiya kuma tabbas masu tasowa zasu musu Alƙalanci kan abubuwan da suka aikata. Ina farin ciki suna yin abinda ya dace ta hanyar neman shawari da tattaunawa."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Meyasa Kwankwaso Ya bar PDP da APC?
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana dalilan da suka ja ya fice daga manyan jam'iyyu a ƙasar nan PDP da APC.
Sanata Kwankwaso ya shiga APC ne bayan ficewa daga PDP a 2013. Ya kuma sake koma wa PDP a 2018 amma ya sake fita a shekarar 2022 ya koma NNPP mai kayan daɗi.
Da yake tsokaci kan haka, ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP yace ya rungumi APC a kokarinsa na kawo wa Al'umma canji, sai dai hakan bai haifar da sakamakon da ake tsammani ba.
"Nima ɗan PDP ne kamar kai a 1998, na samu damar zama ɗaya daga iyayen da suka kafa jam'iyyar. Mun taka rawa musamman a shekaru 8 na farko, lokaci na tafiya abubuwa suka fara lalacewa."
"Hakan ne ya sa muka yanke kawo canji a tsarin siyasar ƙasar nan a 2013/2014, muka kafa APC da yaƙinin zata zama jam'iyyar ci gaba, wacce zata warware matsalolin da suka dami 'yan Najeriya a lokacin."
"Bisa rashin sa'a lokaci na kara tafiya, jam'iyyar ta nuna ta fi PDP muni shiyasa suke kwansu a wuri guda, suna ganin zaɓe zai kasance tsakanin mara kyau da wanda ya fi muni."
- Kwankwaso.
'Yan Daba Sun Kai Farmaki Wurin Gangamin Yakin Neman Zaben Atiku a Gombe
A wani labarin kuma Yan Daban da ake kira 'Kalare Boys' a jihar Gombe sun farwa mutane a wurin gangamin Kamfen Atiku Abubakar
Rahotanni sun tabbatar da cewa aƙalla magoya bayan PDP uku ne suka ji raunuka daban-daban kuma aka lalata ababen hawa guda uku.
An ce lamarin ya faru ne bayan ɗan takarar shugaban kasa ya bar filin tare da yan tawagarsa, amma 'yan sanda sun kai ɗauki da wuri don shawo kan lamarin.
Asali: Legit.ng