Ganduje Ya Kalubalanci Kwankwaso Da Ya Tara Jama'a Kamar Yadda Tinubu Ya Yi a Kano
- Gwamna Ganduje ya caccaki tsohon gwamnan jihar da ke neman gaje kujerar Buhari a zaben 2023 mai zuwa
- Ganduje ya kalubalanci Kwankwaso da ya gwada yin taron gangamin tara mutane miliyan daya a jihar Kano
- Gwamna Wike ya ce Kwankwaso zai samu goyon bayansa duk lokacin da yazo yin kamfen a jihar Ribas
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kalubalanci dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso da ya yi taron gangamin nuna sanuwarsa a jihar Kano.
Da yake magana kai tsaye a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels, Ganduje ya yaba tare da bayyana kwarin gwiwa ga yadda APC ta tara mutum miliyan 1 a Kano don tallata Tinubu.
A karshen makon jiya ne aka gudanar da taron gangami a jihar Kano, inda aka tara dubban masoya APC a jihar don nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasan APC.
Ya shaidawa Channels Tv cewa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Kwankwaso dan takarar shugaban kasa ne, babu shakka a kan haka. Amma duk da haka, muna nan kuma mutane da yawa a yanzu suna tare da jam'iyyar siyasarmu.
"Don haka, idan Kwankwaso yana tunanin zan yi nasara kan jam'iyyar, ya zi ya yi gangamin irin wannan tare kuma ya kwatanta me zai faru idan zai iya."
Dambarwar Shekarau da Kwankwaso
Da yake tsokaci game da dambarwar da ta faru tsakanin Shekarau da Kwankwaso, Ganduje ya ce akwai ayar tambaya game da nagartar jam'iyyar NNPP.
Bayan komawa jam'iyyar NNPP, Kwankwaso ya jawo sanata Ibrahim Shekarau, amma daga baya suka samu sabani bisa wasu dalilai na kujerun siyasa.
Ana yawan samun dambarwar siyasa a kasar nan, musamman tsakanin masu rike da mukamai da wadanda suka gaje su.
Wike zai ba Kwankwaso tallafi
A wani labarin kuma, gwamnan PDP a jihar Ribas ya yaba da yadda tsaron Kwankwaso yake, ya ce zai ba shi tallafin da yake bukata idan yazo gangami jihar.
Nyesom Wike ya ce Kwankwaso ya cancanci mulkar Najeriya, amma kash, yanzu kam ba a jam'iyya daya suke ba.
Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin dan takarar shugaban kasa na PDP da gwamna Wike na jihar ta Ribas.
Asali: Legit.ng