An Ga Taron Matasa Yayin da Seyi Tinubu, Da Ga Dan Takarar APC Ke Jagorantar Gangamin Kamfen a Kano

An Ga Taron Matasa Yayin da Seyi Tinubu, Da Ga Dan Takarar APC Ke Jagorantar Gangamin Kamfen a Kano

  • Dan Bola Ahmad Tinubu, Seyi ya fito a gangamin da aka gudanar a jihar Kano, inda aka ga taron matasa magoya bayan APC
  • Gwamna Ganduje ya ce Kano jihar Tinubu ce, kuma tabbas zai kawo jihar a zaben da za a gudanar a watan Fabrairun 2023
  • Ba wannan ne karon farko da jinin dan takarar shugaban kasa zai fito fili don shiga gangamin zabe ba

Jihar Kano - Seyi, da ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya dura jihar Kano a ranar Lahadi domin jagorantar dandazon masoya mahaifinsa a wani gangamin tallata jam'iyyar.

Daraktan tawagar kamfen Tinubu/Shettima, Baffa Babba Danagundi ya yi bayani game da wannan lamari, inda yace wannan gangami zai yi kira ne ga masoya Tinubu da su tabbatar sun mallaki katin zabe kafin 2023.

Kara karanta wannan

2023: Ganduje Ya Gaza Rufe Bakinsa Ganin Cikar Ƙwarin Matasa, Yace Tinubu Ya Gama da Kano

A hotunan Legit.ng Hausa ta gani daga jaridar The Nation, an ga dandazon jama'a a birnin Kano, lamarin da ya yi sanadiyyar hana wasu masu kasuwanci a yankin tafiyar da lamuransu.

Dan Tinubu ya jagoranci gangamin kamfen a Kano
An Ga Taron Jama’a Yayin da Seyi Tinubu, Da Ga Dan Takarar APC Ke Jagorantar Gangamin Kamfen a Kano | Hoto: The Nation Newspaper
Asali: Facebook

Kano ta Tinubu ce, inji gwamna Ganduje

An tattaro cewa, wannan gangami da APC ta yi ta shirya gangamin mutane miliyan daya masu katin zaben PVC ne a jihar Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya hallara a wannan gangami, ya kuma bayyana cewa, an yi taron ne don nuna goyon baya ga dan takarar da 'yan APC za su zaba a zaben Fabrairun 2023, DailyPost ta ruwaito.

A cewarsa:

"Mun shirya wannan gangamin mutum miliyan daya masu PVC ne domin nuna cewa jihar ta Tinubu ce."

Kalli hotunan:

Mubarak Munkaila, matashi dan jam'iyyar APC a jihar Kano da aka gudanar da wannan gangami tare dashi ya shaidawa wakilin Legit.ng Hausa cewa, ya ji dadin ganin yadda dan takarar shugaban kasan ya turo dansa irin wannan gangami.

Kara karanta wannan

Matasan Jihar Buhari Sun Fara Zuwa Gida-Gida, Sun Yi Wa Tinubu Alkawarin Kuri'u Miliyan a 2023

A cewarsa:

"A baya da wahala ka ga dan dan siyasa a cikin matasa 'ya'yan talakawa suna yawo a rana da sunan kamfen, yanzu kuma mun ga bambanci, dan Tinubu ne ya jagorance mu.
"Za mu yi mahaifinsa a 2023 ba tare da la'akari da kudi ba, ba ma bukatar komai, kawai yadda ya nuna yana yinmu matasa shi ya burge mu."

A wannan shekarar, 'yan siyasa na damawa da 'ya'yansu a lamuran da suka shafi kamfen, musamman a wasu bangarori da matasa ke iya bi.

Diyar Atiku ta fito a jerin masu kamfen gabanin zaben 2023

A baya kunji cewa, diyar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ta fito a jerin masu gangamin kamfen dinsa na zaben 2023 mai zuwa.

A rahoton da muka samo, Hauwa Atiku-Uwais za ta jagoranci majalisar matasa wajen gangamin kamfen na neman zaben mahaifinta gabanin zaben 2023.

Jerin da aka fitar na kwamitin majalisar matasan ya bayyana sunayen jiga-jigan matasa a Najeriya da za su jagoranci tafiyar, diyar Atiku ce shugaba.

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.