Majalisar Malamai da Limamai sun fito da ‘Dan takaran Shugaban Kasarsu a Zamfara
- Kabiru Marafa ya zauna da majalisar malamai, limamai, ladanai da mataimakansu da ke Zamfara
- Malaman addinin Musuluncin sun sha alwashin goyon bayan jam’iyyar APC a zaben da za a shirya a 2023
- A jawabin da ya fitar, Sakataren yada labaran APC na Zamfara ya tabbatar da cigaban da jam’iyyar ta samu
Zamfara - Majalisar malaman addinin Musulunci sun nuna za su goyi bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Gwamna a jihar Zamfara a zaben 2023.
Daily Trust ta rahoto cewa malaman za su marawa ‘yan takaran jam’iyyar APC mai mulki baya.
Wadannan manyan malamai sun yabawa gwamnatocin Bello Matawalle a jihar Zamfara da kuma Mai girma Shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya.
Majalisar malaman tayi wannan alkawari ne a wajen wani zama da suka yi da shugaban yakin neman zaben Tinubu/Shettima, Kabiru Garba Marafa.
Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Omo Ovie-Agege Yace Shine Ya Dakatar da Kudirin Tsige Shugaba Buhari
Sanata Kabiru Garba Marafa ne shugaban kwamitin da yake taya Bola Ahmed Tinubu neman zama shugaban Najeriya a karkashin APC a jihar ta Zamfara.
Malamai da Limamai sun gamsu da APC
Leadership tace shugaban majalisar malaman Zamfara, Sheikh Abubakar Fari da Muhammad Dan-Alhaji sun yi jawabi a madadin shehunan da ke jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Liman Muhammad Dan-Alhaji shi ne shugaban kungiyar Limaman Juma’a, kuma shi ne limamin da ke jagorantar babban masallacin Juma’a na Gusau.
Malaman sun bayyana cewa sun gamsu Bola Tinubu mai neman zama shugaban kasa a karkashin APC shi ne ‘dan takaran da ya fi cancanta da mulki.
Bola Tinubu ya yi an gani
Sanata Marafa ya roki malaman musuluncin da limamai da ladanai da na’ibansu da su goyi bayan Bola Tinubu saboda an ga irin ayyukan da ya yi a baya.
A rahoton da Vanguard ta fitar, an ji Marafa yana yabawa Tinubu, yace ya yi ayyukan da za a yaba a lokacin da ya yi gwamnan Legas daga 1999 zuwa 2007.
Tsohon Sanatan na Zamfara ta tsakiya, yace idan Tinubu ya zama shugaban Najeriya, zai maimaita irin cigaban da ya kawo a Legas ta fannin tattali da walwala.
Sakataren yada labaran jam’iyyar APC mai mulki na reshen jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya tabbatar da haka a wani jawabi da ya fitar a makon nan.
Da wahala PDP ta ci zabe - Fayose
An samu labari Ayodele Fayose yace Jam’iyyar PDP tana yaudarar kanta, ba za tayi nasara a jihohin da suke Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma ba.
‘Dan adawar yace dole a sasanta da Gwamnonin da ke tare da Nyesom Wike, kuma ayi sulhu da Peter Obi kafin Atiku Abubakar ya iya lashe zaben 2023.
Asali: Legit.ng