Shugabannin Jam’iyyar APC Sun Ce Ba Su Goyon Bayan 'Dan Takaran Gwamnansu
- Shugabannin jam’iyyar APC na reshen jihar Abia, sun ce ba za su goyi bayan takarar Dr. Uche Ogah ba
- Uche Ogah shi ne wanda ya yi nasara a kotu, Alkali ya tsaida shi a matsayin ‘dan takaran Gwamna a Abia
- Tsohon Ministan ya samu matsala daga cikin gidan APC, masu rike da jam’iyya suna tare da Ikechi Emenike
Abia - Shugabannin jam’iyyar APC na reshen jihar Abia, sun nuna ba za su marawa Uche Ogah baya a zaben Gwamna da za a shirya a shekarar badi ba.
Vanguard ta rahoto shugaban APC a Abia, Dr. Kingsley Ononogbu yana cewa ba su tare da Dr. Uche Ogah wanda kotu ta ayyana a matsayin ‘dan takara.
Kingsley Ononogbu yace a lokacin da Ogah ya samu nasara a shari’ar da aka yi a Abuja, shi kadai ya yi bikin murna ba tare da shugabannin jam’iyya ba.
Shugaban APC na jihar Abia yace wannan ya nuna babu ruwan jagororin jam’iyya da takarar kujerar Gwamnan da tsohon Ministan yake yi a zaben badi.
Allah ya raka taki gona - Ononogbu
"Abin mamaki Uche Ogah da ya maida shari’arsa zuwa Abuja saboda matsalar tsaro a Abia, ya sake dawowa jihar ta Abia domin murnar nasarar da yake tunanin ya yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai murnar, Uche Ogah ya nuna bai kaunar mutanen Abia, kuma bai damu da halin da suke ciki a gwamnatin jam’iyyar PDP mai mulki ba.
Ogah yana kokari ne wajen taimakawa wadanda suke mulki wajen ganin sun cigaba da rike jihar.
Abin da ya sa duk wani babba a jam’iyyarmu ya nesanta kan shi daga Ogah shi ne duk san dabararsa, kuma ba su goyon bayan irin tafiyarsa
Ya zo da wani nuku-nuku a lokacin da jam’iyyarmu ta shirya da kyau domin ceto da kawo cigaba a Abia."
- Dr. Kingsley Ononogbu
A cewar shugaban na APC, Ogah da mutanensa sun zo ne domin su ruguza jam’iyyar adawar, yace ‘dan takaran bai da nauyin da zai tabuka abin kirki a zabe.
Ni ne wanda zai iya cin zabe - Ogah
Sun ta rahoto tsohon Ministan tarayyan yana kira ga magoya bayansa a Umuahia cewa shi ne wanda zai iya kawowa APC nasara a zaben Gwamnan jiha.
Amma Jagororin APC na kasa da na reshen Abia irinsu Sir Friday Nwosu da Chidi Avajah duk sun nuna Ikechi Emenike suke goyon baya ba Uche Ogah ba.
Kowa yana tare da Tinubu
A matakin kasa kuwa, an samu rahoto cewa Jos ta cika makil, kusan duk wani babba a jam’iyyar APC, ya halarci kaddamar da yakin zaben da aka yi.
Shugaba Muhammadu Buhari, Gwamnonin jihohi, Shugabannin majalisa, tsofaffin Ministoci da Gwamnoni suna jihar Filato a ranar Talatar da ta wuce.
Asali: Legit.ng