2023: Gwamnoni 5 Sun Gama Shirin Ficewa Daga PDP? Kwamitin Kamfen Atiku Ya Faɗi Gaskiya

2023: Gwamnoni 5 Sun Gama Shirin Ficewa Daga PDP? Kwamitin Kamfen Atiku Ya Faɗi Gaskiya

  • Tawagar yakin neman zaɓen shugaban kasa a inuwar PDP ta musanta jita-jitar cewa tsagin Wike na shirin ficewa daga jaam'iyyar
  • Chief Dele Momodu, Daraktan sadarwa ya musanta jita-jitar da cewa ba ta yadda za'ai su sauya sheka ba su sanar ba
  • Yace kwamitin kamfen tsohon mataimakin shugaban kasa ya jingine duk wani rikici ya tukari babban zaɓen 2023

Kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ya musanta raɗe-rafin dake yawo cewa tawagar gwamnonin nan 5 watau G5 sun fice daga jam'iyyar PDP.

Daraktan sashin sadarwa na kwamitin, Chief Dele Momodu, shi ne ya tabbatar da haka yayin zantawa da manema labarai a Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Dataktan Sadarwa, Dele Momodu.
2023: Gwamnoni 5 Sun Gama Shirin Ficewa Daga PDP? Kwamitin Kamfen Atiku Ya Faɗi Gaskiya Hoto: thenation
Asali: UGC

Momodu ya yi wannan ƙarin haske ne bayan ganin jagoran G5 kuma gwamnan Ribas, Nyesom Wike, yace zai tallafa wa ɗan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Atiku Ko Tinubu? Daga Karshe, Tsohon Gwamna Na Hannun Daman Wike Ya Faɗi Wanda Zai Goyi Baya a 2023

Wike, wanda ya gayyaci Obi ya kaddamar da gada a Ribas ranar Alhamis, ya tabbatar masa da zai taimaka masa da kayayyaki duk randa ya zo Ribas kamfe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake fatali da raɗe-raɗin, Dele Momodu yace gwamna Wike da sauran yan tawagarsa hudu, duk da fuashin da suka yi ba zasu bar PDP ba tare ɗa sun sanar ba.

Yace:

"Game da batun gwamnonin G5 ba wahayi ake mun ba, bani da masaniya ko sun bar jam'iyya ko suna nan. Duk ranar da suka fice PDP zasu sanar kuma zamu sani, amma a yanzu suna nan cikin PDP."
"Har yanzun akwai ƙofar yin sulhu, abinda suke ta nanatawa shi ne ba su jin daɗi kuma zamu ci gaba da rokon Allah ya dawo da zaman lafiya a cikin gida."

Momodu ya bayyana cewa tawagar yakin neman zaɓen Atiku ta maida hankali kan harkokin siyasa kana ya jaddada cewa ba abinda zai ɗauke musu hankali.

Kara karanta wannan

'Na Maka Magiya Dan Allah' Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Roki Wike Ya Goya Masa Baya a 2023

Tsagin Gwamna Wike Sun Gindaya Sharudda a Sabon Shirin Sulhu da Atiku

A wani labarin ɓangaren tawagar gwamnonin G5 na PDP sun ce zasu karbi sulhu ne kawai idan za'a yi adalci, gaskiya da dai-daito

Shugaban tafiyar kuma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace a shirye suke a zauna a yi sulhu kan sharuddan da suka kafa.

Yace abun mamamkin shi ne mutane dake yabonsa jiya sune kuma yau suka ɗauke shi abokin gaba don kawai yace an yi ba dai-dai ba a gyara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262