Yan Kasuwa Daga Yankin Inyamurai Sun Tarawa Tinubu Biliyan Daya Don Kamfen Din Zaben 2023

Yan Kasuwa Daga Yankin Inyamurai Sun Tarawa Tinubu Biliyan Daya Don Kamfen Din Zaben 2023

  • Kungiyar yan kasuwa daya yankin kudu maso gabas sun yiwa Asiwaju Bola Tinubu sha-tara ta arziki gabannin babban zaben 2023
  • Yan kasuwar kimanin su dubu biyun sun yi karo-karo na naira biliyan daya domin dan takarar shugaban kasar na APC ya samu yayi kamfen a zabe mai zuwa
  • Tinubu ya dauki alkawarin yin adalci a mulkinsa ta yadda dukkanin yan Najeriya za kwankwadi romon damokradiya ba tare da nuna banbanci ba

Yan kasuwa kimanin su 2,000 daga yankin kudu maso gabas sun yi bayar da gudunmawar naira biliyan daya domin tallafawa yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Hope Uzodimma ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba a yayin wani taro tsakanin Tinubu da shugabannin yan kasuwa a yankin, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Tono Wani Abu a Bangaren Tsaro a Mulkin Buhari, Yace Ba Zai Haka Ba Idan Ya Ci Zabe

Bola Tinubu
Yan Kasuwa Daga Yankin Inyamurai Sun Tarawa Tinubu Biliyan Daya Don Kamfen Din Zaben 2023 Hoto: @Official_ABAT
Asali: Twitter

Uzodimma ya bayyana cewa mambobin kungiyar sun fito ne daga jihohi biyar na yankin kudu maso gabashin kasar.

Yan kasuwar sun fadi abun da suke so Tinubu yayi masu

Wani mai magana da yawun kungiyar, Emeka Mgbudem ya ce kungiyar ta yarda da Najeiya kuma tana son zaman lafiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mgbudem ya ce mambobin kungiyar sun yi karo-karo na N500,000 kowannensu saboda sun yarda da Tinubu, bayan sun karanta manufofinsa ga Najeriya.

Ya ce a duk inda dan kabilar Ibo ya saka kudinsa, ya zaka zuciyarsa ne.

Sai kuma ya bukaci Tinubu da ya cire shingaye da yawa da ke kan hanyoyi a yankin sannan ya gina hanyoyi da ke sada manyan biranen jiha a yankin.

Tinubu ya daukarwa yan kasuwar alkawari

Da yake martani, Tinubu ya dauki alkawarin samar da fasaha wajen tantance kayayyaki a tashoshin jiragen ruwa wanda zai kawar da shingaye marasa kan gado a kan hanyoyi, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Yadda Gwmanan Jihar Ebonyi Ya Nuna Gyan Bayan Karara Ga Dan Takarar Jami'iyyar APC

Ya kuma yi alkawarin tafiyar da gwamnati inda za a nuna daidaito wajen kula da dukkanin yan Najeriya.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamna Dave Umahi ya nuna goyon bayansa ga tafiyar Bola Tinubu a babban zaben 2023 mai zuwa.

Umahi ya ba tsohon gwamnan na jihar Lagas tabbacin cewa mutanen jihar Ebonyi shi za su yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel