2023: Na Gano Matsalar Najeriya Kuma Zan Magance Ta, Peter Obi

2023: Na Gano Matsalar Najeriya Kuma Zan Magance Ta, Peter Obi

  • Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, yace ya san matsalar Najeriya kuma yana da hanyoyin magance ta
  • Ɗan takarar shugaban kasan yace babban abinda ke damun Najeriya shi ne rashin iya sarrafa kayayyaki, ya jero abinda zai yi
  • Peter Obi ya ziyarci jihar Ribas ne domin kaddamar da gadar sama bayan gwamna Wike ya gayyace shi

Rivers - Ɗan takarar shugaban kasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, yace ya gano asalin tushen matsalar da ta addabi ƙasar nan.

Mista Obi ya yi wannan furucin ne a jihar Ribas ranar Alhamis yayin da Gwamna Wike ya gayyace shi ya kaddamar da gadar Nkpolu-Oroworokwo, ta Tara da gwamnatin Ribas ta gina a mulkin Wike.

Peter Obi da Wike.
2023: Na Gano Matsalar Najeriya Kuma Zan Magance Ta, Peter Obi Hoto: Peter Obi, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Peter Obi ya bayyana babbar matsalar Najeriya da cewa ƙasar bata sarrafa kayakki a cikin gida.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnan PDP ya yi watsi da Atiku, ya zabi dan takarar da zai taimakawa a jiharsa 2023

Yace ya gudanar da kwarya-kwaryan bincike kuma a yanzu ya san abinda kowane yankin ƙasar nan ke bukata wanda zai amfani mutane, ya kuma jaddada kudirinsa na gyara Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa yace:

"Na san matsalar ƙasar nan, abu ɗaya ne, Najeriya bata iya samar da komai. Na sha faɗa lokuta da dama kuma zan sake faɗa cewa na san abinda zai zama mai amfani ga dukkan sassan ƙasar nan."
"Na faɗa musu a arewa lokacin da muka gudanar da gamgamin kamfe cewa zamu inganta ƙasarsu ta noma. Suna da ƙasa mu kuma zamu inganta amfaninta."
"Kudu maso yamma zata zama cibiyae samun kuɗaɗenmu, gabashi kuma ya zama Cibiyar mana'antunmu. Zamu sake fasalin Tashar ruwan Ribas ta yadda zamu rika fitar da kayanmu ta nan."

Ɗan takarar shugaban ƙasan, wanda ya samu tarba daga dandazon mutane a Patakwal, ya roki mazauna Ribas su ɗauke shi kamar ɗaya daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Mutanen Jihata Zasu Angiza Wa Tinubu Tulin Kuri'unsu, Atiku Bai da Rabo, Gwamna Ya Magantu

Mun tare da kai - Wike

A jawabinsa, Gwamna Nyesom Wike, ya sha alwashim taimaka wa kamfen Peter Obi a Ribas da kyayyaki.

Yace, "Duk lokacin da zaka yi kamfe ka sanar da ni, duk wani taimako na kayayyaki zamu baka. Na sanka, na san kana da duk abinda ake bukata na jagorancin ƙasar nan, ba mai musu."

A wani labarin kuma Tsagin Gwamna Wike G5 Sun Gindaya Sharudda a Sabon Shirin Sulhu da Su Atiku Abubakar, Ayu

Jagoran gwamnonin G5 kuma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace basu gudun a yi sulhu a APC amma bisa sharuddan da suka fafutuka a kai.

Da yake jawabi a wurin kaddamar da wafa gada da gwamnatinsa ta gina, yace duk zaman da za'ai dole a gina shi kan adalci da daidaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262