INEC Za Ta Gana da Gwamna Ganduje da Ortom Don Tattauna Batun da Ya Shafi Zaben 2023

INEC Za Ta Gana da Gwamna Ganduje da Ortom Don Tattauna Batun da Ya Shafi Zaben 2023

  • Hukumar zabe mai zaman kanta za ta tattauna da jiga-jigan siyasar kasar nan kan batutuwan da suka shafi zaben 2023
  • An gayyaci wasu gwamnoni, dan takarar shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki na kasar nan
  • Majiya ta bayyana maudu'in da za a tattauna a kai don shawo kalubalen tsaro a zaben 2023 mai zuwa badi

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a ranar Talata mai zuwa za ta gana da gwamnoni, jami'an tsaro da dan takarar shugaban kasa gabanin zaben 2023 mai zuwa nan kusa.

Za a yi tattaunawar ne a Nicon Luxury a birnin tarayya Abuja tare da kwamishinan INEC kan harkokin wayar da masu kada kuri'u, Festu Okoye, Punch ta ruwaito.

A bangaren 'yan siyasa, za a zauna da gwamna Abdullahi Ganduje na Kano, gwamna Bala Muhammad na Bauchi da gwamna Samuel Ortom na jhar Benue.

Kara karanta wannan

'Na Maka Magiya Dan Allah' Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Roki Wike Ya Goya Masa Baya a 2023

INEC za ta zauna da jiga-jigan siyasar kasar nan
INEC Za Ta Gana da Gwamna Ganduje da Ortom Don Tattauna Batun da Ya Shafi Zaben 2023 | Hoto: guardian.ng
Asali: Twitter

A bangaren hukumomin tsaro, za a yi zaman tare da sufeta janar na 'yan sanda, Usman Alkali Baba da dai sauransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, za a yi da dan takarar shugaban kas ana jam'iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, shugaban majalisar zauren shawarin jam'iyyun siyasa, Yabagi Sani, kungiyar 'yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki a harkar zabe.

Yadda aka shirya gudanar da taron

Wannan batu dai na fitowa ne a cikin wata sanarwa da wanda ya shirya zaman, Edwin Olofu ya fitar a ranar Laraba 16 ga watan Nuwamba, Daily Trust ta ruwaito.

Olofu, wanda kuma shine manajan daraktan jarida Platinum Post ya bayyana cewa, wadanda za su halarci zaman za su tafka muhawara ne kan yadda za a yi zabe cikin lumana a badi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, Hamza Al-Mustapha zai yi fashin baki kan maudu'i matsalolin na zamani da kalubalensu da kuma illar hakan ga zaben 2023.

Kara karanta wannan

Jerin Bukatu 7 Da CAN Ta Gabatarwa Tinubu: Bukatu 2 Da Zai Yiwa Tinubu Wahalan Biya

CAN ta yi zama da Bola Ahmad Tinubu

A wani labarin na daban, a kokarin gano inda ake da matsala a kasar da kuma neman mafita da kare muradun Kiristocin Najeriya, CAN ta gayyaci Tinubu don tattaunawa ta musamman.

Kungiyar ta kuma gayyaci sauran 'yan takarar shugaban kasa domin shaida musu abin da take so a yi mata bayan zaben badi.

A baya an samu rashin jituwa tsakanin Tinubu d akungiyar kiristocin Najeriya saboda ya zabi Musulmi a matsayin abokin takararsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.