Rikicin PDP: Tsagin Gwamna Wike Sun Gindaya Sharudda a Sabon Shirin Sulhu da Atiku
- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jaddada cewa bukatar G5 shi ne a zauna a yi dai-daito, da adalci a jam'iyyar PDP
- Wike wanda ya ja daga da shugabancin PDP, yace yana mamakin yadda a baya komai sai da Wike amma yanzun kuma ana masa kallon makiyi
- A cewarsa, mutanen da ke yabonsa a baya yanzun saboda ya nemi a gyara kuskure suna masa kallon ɗan tada yamutsi
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jaddada cewa tawagar gwamnonin PDP G5 zasu zauna a yi sulhu ne kawai kan dai-daito, adalci da gaskiya.
Wike ya faɗi haka ne a wurin kaddamar da katafariyar gadar sama Rumuepirikom, gada da Takwas da gwamnatin Ribas ta kammala ginawa a mulkinsa.
Daily Trust tace tsohon shugaban APC na ƙasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, ne ya kaddamar da gadar ranar Laraba 16 ga watan Nuwamba, 2022.
Da yake jawabi a wurin, Wike yace wasu mambobin jam'iyyar basu da aikin da ya wuce yaba masa da sauran takwarorinsa na G5 a baya amma yanzu sun juya baya suna kiransu da wasu sunaye don kawai sun ce a gyara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnan ya ce:
"Ina da tabbacin kafin yanzu waɗannan mutanen da kuke gani a jam'iyya basu iya cewa uffan ba tare sun ambaci Wike ba. Amma yanzu saboda nace an yi kuskure a dawo a gyara, yanzu na zama abokin gaba."
"Sune fa mutanen da a baya suke yabo na dare da rana a kowace rana, amma don kawai nace ku tsaya muna da yarjejeniya, mu zauna mu cikata, wasu suka fara ganin ba za'ai ba, mu kuma mun kafe sai an yi."
"(Sharuddan mu abune mai sauki) Mun tsaya kan dole a yi adalci, dai-daito da gaskiya. Wannan ne abinda G5 zata ci gaba da fafutuka akai. Bamu ƙi a yi sulhu ba, amma sulhun dole ya hau kan adalci, dai-daito da gaskiya."
Bayan haka, Wike ya kara da bayyana cewa ba zai taɓa goyon bayan wanda baya son jiharsa kuma baya kaunar cigabanta ba.
Nan Ba Da Jimawa ba Atiku Da Wike Zasu Shirya, Saraki
A wani labarin Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, yace nan gaba kaɗan jama'ar Najeriya zasu sha mamaki game da PDP
Da yake jawabi a wurin addu'ar cikar mahaifinsa shekara 10 da rasuwa, Saraki yace rigingimun PDP na gaba da zuwa ƙarshe kuma mutane zasu sha mamaki
Tsohon gwamnan Kwara yace ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen kokarin sa farin ciki a zuƙatan mutane da tsayuwa kan gaskiya a kowane hali.
Asali: Legit.ng