Manyan Kudu maso Kudu Sun Fara Shirye-Shiryen Karya Bola Tinubu a Zaben 2023
- Manyan kasa da kungiyoyi da-dama da ke Neja-Delta za su fadawa mutanensu wanda za su zaba 2023
- Kungiyar ARNDR za tayi la’akari da ‘yan takaran shugaban kasa, sai ta fadi wanda ya dace a goyi bayansa
- Alamu na nuna kungiyar ba ta tare da Bola Tinubu saboda tsare-tsaren da Gwamnatin APC ta zo da su
Niger Delta - Dattawa, masu ruwa da tsaki, gamayya da kungiyoyin kwararru a Neja-Delta sun fara wayar da kan al’umma a game da zaben shugaban kasa.
Vanguard tace an fara wannan ne biyo bayan wasu jerin tarurruka da aka yi a yankin, inda aka koka da kamun ludayin gwamnatin Muhammadu Buhari.
Dattawa, manyan kasa da sauran masu ruwa da tsaki a kan al’amuran Neja-Delta sun narke cikin wata kungiya mai suna ARNDR da za ta budewa jama’a ido.
Manufar ARNDR ita ce tsayawa mutanen bangarenta domin zaben wanda ya dace a 2023.
James Komobila ya fitar da jawabi
Jaridar tace Mai magana da yawun wannan kungiya, James Komobila ya fitar da jawabi kwanaki, ya nuna ARNDR ba ta goyon bayan takarar Bola Tinubu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dalili kuwa shi ne yadda gwamnatin APC mai-ci tayi watsi da al’amarin Neja-Delta a tsawon shekaru bakwai da Muhammadu Buhari yake rike da Najeriya.
Komobila ya nuna cewa gwamnatin PDP ta kawo tsare-tsaren da suka taimakawa bangarensu, yace ana neman watsi da wadannan a gwamnatin APC.
Zunuban APC da shirin Umahi
A lokacin mulki PDP ne aka kafa hukumomin NDDC da NCDMB, aka kawo tsarin afuwa na PAP, kuma aka ware karin kason 13% ga jihohi masu man fetur.
A rahoton Sun, kungiyar ta zargi gwamnati mai-ci da bata lokaci wajen kafa majalisar da za ta rika kula da kuma sa ido a kan aikin hukumar NDDC.
Yayin da ARNDR take cewa za ta duba matsayar da za ta dauka game da 2023, Gwamna David Umahi yace mutanen jiharsa za su zabi Bola Tinubu ne.
A matsayinsa na Gwamna a APC, Umahi zai taimakawa jam’iyyarsa. Takarar Tinubu za ta fuskanci kalubale musamman daga Atiku Abubakar da Peter Obi.
Babu batun addini ko kabila a 2023 - Wike
Da ya gayyaci tsohon Shugaban APC na kasa watau Adams Oshiomhole, an ji labari Mai girma Gwamnan Ribas ya yi maganar yadda 2023 za ta kasance.
Nyesom Wike yana ganin babu dalilin da za a ki zaben ‘dan takara saboda ba a gamsu da yankin da ya fito ba ko kuma addinin da ya yi imani da shi.
Asali: Legit.ng