Buhari Ya Ɗaga Darajar Najeriya Har Ta Wuce Manyan Kasashen da Suka Cigaba, Bello

Buhari Ya Ɗaga Darajar Najeriya Har Ta Wuce Manyan Kasashen da Suka Cigaba, Bello

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yace mulkin Buhari ya ɗaga darajar Najeriya ta zarce ƙasashe da dama har da na cigaba
  • Da yake jawabi a Jos wurin kamfen Tinubu, Bello yace shugaba Buhari ya yi aikin azo a gani a mulkinsa ta kowane fanni
  • Ko'odinetan matasa na kamfen Tinubu ya ƙara da cewa ba zai huta ba har sai ya gamsar da matasa sun zabi APC a 2023

Jos, Plateau - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, yace karkashin mulkin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Najeriya ta zarce wasu ƙasashen da ake cewa sun ci gaba.

The Cable tace Bello ya yi wannan furucin ne a wurin gangamin fara yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Rwang Pam township stadium Jos, babban birnin jihar Filato.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Buhari Ya Ɗaga Darajar Najeriya Har Ta Wuce Manyan Kasashen da Suka Cigaba, Bello Hoto: Governor Yahaya Bello
Asali: Facebook

Sai dai gwamnan bai ambaci sunayen ƙasashen da suka riga suka cigaba, waɗanda yake nufin a mulkin Buhari Najeriya ta wuce da ajinsu ba.

Kara karanta wannan

2023: Atiku da Tinubu Sun Kara Shiri, Sun Yi Sabbin Naɗe-Naɗe a Kwamitin Yakin Neman Zabe

Gwamna Bello yace shugaba Buhari ya yi abinda ya kamata a mulkinsa, inda yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ka yi kokari a ɓangaren ayyukan raya ƙasa da tattalin arzikinmu. Ka karɓi ƙasar nan lokacin da aka samu koma bayan tattalin arziki da ƙalubale a faɗin duniya. Yau a Najeriya mun wuce ajin wasu ƙasashe harda waɗanda suka cigaba."
"A mulkin APC ne ka baiwa mata da matasa masu naƙasa dama. Ranka ya daɗe ka yi abin azo a gani daga 2015-2019 haka nan daga 2019 zuwa yau kuma zaka miƙa wa Tinubu domin ya ɗora kamar yadda ya yi a Legas."

Zan jawo matasan ƙasar nan su zaɓi Tinubu - Bello

Gwamna Bello ya ƙara da cewa a matsayin Kodinetan matasa, zai haɗo kan matasa a lungu da sakon ƙasar nan su zaɓi Bola Ahmed Tinubu a 2023.

Kara karanta wannan

'Ramuwar Gayya Muka Yi': Kotu Ta Yanke Wa Wasu Makiyaya Uku Hukunci Kan Ƙone Gonar Gyaɗa Ta Miliyan N1.5m

"Ina mai tabbatar da cewa duk wani matashi da zai fita runfar zaɓe zai je ne domin mu. Ba wai don Tinubu, Shettima ko Buhari ba, sai domin karan kan mu, matasa da waɗanda ba su shigo duniya ba."

Mambobin PDP Sama da 12 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Ƙaduna

A wani labarin ɗan takarar gwamnan Kaduna a inuwar APC, Malam Uba Sani, yace babu sauran ɓurɓushin PDP a ƙaramar hukumar Giwa

Da yake karban dubbannin masu sauya sheƙa, Sanata Uba Sani ya nemi mutanen su yi aiki tukuru don nasarar APC tun daga sama har ƙasa.

An tattaro cewa, tsohon kwamishina, jiga-jigai da mambobin PDP sama da 12,000 ne suka tattara kayansu zuwa jam'iyyar APC a yankin Guwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel