2023: Zan Maida Wani Dan Takarar Shugaban Ƙasa Mahaifarsa da Ya Gudo, Tinubu

2023: Zan Maida Wani Dan Takarar Shugaban Ƙasa Mahaifarsa da Ya Gudo, Tinubu

  • Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, yace zai maida ɗan takarar LP, Peter Obi jihar Anambra a 2023
  • Ɗan takara a inuwar APC, yace takwaransa na Labour Party yanzu haka a Legas yake zaune bai san hanyar zama shugaban kasa ba
  • Tinubu ya kuma tabbatarwa yan Najeriya cewa fata mai kyau ya dawo, Najeriya zata tsira a hannunsa

Jos, Plateau - Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC, Bola Tinubu, yace takwaransa na LP, Peter Obi, bai san hanyar zuwa kujerar shugaban ƙasa ba a Najeriya.

Tinubu ya yi wannan ikirarin ne yayin da yake jawabi a wurin gangamin fara kamfe ɗinsa yau Talata a Rawang Pam Township Stadium dake Jos, jihar Filato.

Bola Tinubu.
2023: Zan Maida Wani Dan Takarar Shugaban Ƙasa Mahaifarsa da Ya Gudo, Tinubu Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

Yace, "Peter Obi, haaaa wai Obidient, a Legas yake zaune ba a Anambra ba. Bai ma san hanya ba, zamu maida shi Anambra (mahaifarsa)."

Kara karanta wannan

Ali Nuhu, da Wasu Jaruman Kannywood da Nollywood Sun Halarci Kamfen Tinubu, Sun Bada Nishaɗi

Vanguard ta tattaro cewa Tsohon gwamnan wanda ya yi ikirarin cewa Peter Obi ya gudu zuwa Legas ya sha alwashin kora shi zuwa gida a zaɓen 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jagoran APC na ƙasa ya tabbatar wa yan Najeriya cewa fatan da suke ya dawo, inda ya bayyana cewa Najeriya zata wayi gari ta rabu da dukkanin wahalhalun da take fama da su.

A kalamansa yace, "Fata nagari ya dawo, Najeriya zata samu lafiya, ƙasarmu zata daina tangal-tangal, muna ƙara jaddada kudirinmu na kafa shugabanci mai kyau da zai kawo cigaba."

Jiga-jigan da suka halarci gangamin

Taron buɗe yakin neman zaɓen ya samu halartar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, gwamnonin APC da masu ruwa da tsaki.

Sakonnin fatan alheri sun cigaba da karaɗe ko ina yayin da yanzu haka ake cigaba da taron kaddamar da fara yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Jos, rahoton dailytrust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: A Mulkin Buhari Najeriya Ta Kere Wasu Kasashen da Suka Cigaba, Gwamnan Arewa

Gwamnoni da suka haɗa da Yahaya Bello na Kogi, Nasir El-Rufai na Kaduna, Ben Ayade na Kuros Riba, Mala Buni na Yobe, Muhammed Badaru na Jigawa duk sun ce zasu yi aiki don nasarar APC.

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya baiwa ma'aikatan jiharsa hutun kwana ɗaya saboda gangamin APC a Jos

A wata sanarwa, Lalong, wanda shi ne Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaben Tinubu/Shettima, yace za'a samu cunkoso sosai, shiyasa ya ɗauki matakin ba da hutun

Yace zuwan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da sauran manyan mutane zai tsayar da lamurra da dama, don haka yau Taƙata kowa ya huta a gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel