Mutanen Ebonyi Zasu Yi Tururuwar Zaben Bola Tinubu a 2023, Gwamna Umahi
- Gwamnan Ebonyi ya sha alwashin cewa baki ɗaya mutanen jiharsa zasu dangwala wa Bola Tinubu a 2023
- Dave Umahi, ya tabbatar wa ɗan takarar APC cewa zai ga aikin Injiniya duk ranar da ya je Kamfe jihar Ebonyi
- Yace a madadin gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya sun yanke mara wa Tinubu baya domin zai kula da mutanen yankin
Abuja - Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya tabbatarwa ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu, cewa jiharsa zata ba shi ƙuri'u masu yawa a 2023.
Umahi ya yi wannan furucin ne a wurin kaddamar da gidan saukar gwamnan Ebonyi a Abuja ranar Laraba, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Ya kuma bayyana cewa jihar da ke shiyyar kudu maso gabashin Najeriya na shirya masa wani gagarumin gangamin yakin neman zaɓen shugaban kasa.
A ruwayar Vanguard, Umahi yace:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Zamu shirya gangamin da ba'a taɓa gani ba a kudu maso gabas a jihar Ebonyi kaɗai. Duk wata jam'iyya da ta iya samun kashi 10 na kuri'un mutanenmu zamu ƙara musu da wasu saboda ba jam'iyyar da zata iya."
"Saboda haka muna maraba da Tinubu da sauran gwamnonin zuwa jihar Ebonyi wurin uwar gangami. Ranka ya daɗe zaka ga abinda Injiniya zai iya yi idan ka zo.
Baki ɗaya kuri'un Ebonyi naka ne - Umahi
"Bamu ɓoye cewa kai ɗan takararmu ne kuma zaka kula da mutanen kudu maso gabas, kuri'unmu duka na APC ne babu tantama a kan haka, mutanen kudu maso gabas sun ɗau matsaya."
"Ni ne shugaban ƙungiyar gwamnonin kudu maso gabas, ina magana ne a madadin su, mun san hanyar da zata ɓulle mana a 2023 kuma ita ce APC."
- Dave Umahi.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa taron ya samu halartar tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu da wasu mambobin jam'iyya mai mulki.
A wani labarin kuma daga wurin gangamin kamfen Tinubu na Jos, Yahaya Bello ya sha alwashin tattara wa Tinubu matasan Najeriya a zaɓen 2023
Da yake nasa jawabin, gwamnan jihar Kogi, Ko'odinetan matasa, yace mulkin APC tun zuwam Buhari ya ɗaga daraja da ƙimar Najeriya a idon duniya
Gwamnan yace sakamakon ayyukan raya ƙasa da shugaba Buhari ya aiwatar, Najeriya ta kere ƙasashe da dama ciki harda waɗanda suka cigaba.
Asali: Legit.ng