Wani Lauya Ya Jikawa APC Aiki Sharkaf, Ya Garzaya Kotu Zai Yi Shari’a da Bola Tinubu

Wani Lauya Ya Jikawa APC Aiki Sharkaf, Ya Garzaya Kotu Zai Yi Shari’a da Bola Tinubu

  • Mike Enahoro-Ebah ya shigar da wasu kararraki, zai yi shari’a da Asiwaju Bola Tinubu a Kotu
  • Wannan Lauya da ke Abuja yana zargin ‘Dan takaran APC da yin karya a game da shekarunsa
  • Enahoro-Ebah yana tuhumar Tinubu da badakalar satifiket, ba a fara sauraron shari’ar ba

Abuja - Wani lauya mai aiki a garin Abuja, Mike Enahoro-Ebah yana karar Asiwaju Bola Tinubu mai neman zama shugaban kasa a jam’iyyar APC a 2023.

This Day tace Mike Enahoro-Ebah yana zargin Asiwaju Bola Tinubu da yin karya a game da asalin shekarunsa da zargin karyar takardun shaidar karatu.

Lauyan yana kuma tuhumar ‘dan takaran da yi wa hukuma rantsuwa kan karya. An shigar da kararraki uku mabambanta a kotun majistare a Wuse Zone 6.

An shigar da kararrakin masu lamba CR/121/2022, CR/122/2022 da CR/123/2022 a ranar 10 ga watan Nuwamba, Bola Tinubu ne kadai wanda zai kare shi.

Kara karanta wannan

Sanata Binani vs Nuhu Ribadu : Kotu Daukaka Ta shirya yanke hukunci kan zaben fidda gwanin jihar Adamawa

Takardu da shekarun bogi

A kara mai lamba CR/121/2022, za ayi shari’a da tsohon gwamnan na Legas bisa zargin amfani da satifiket na bogi na jami’ar jihar Chicago a Amurka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Enahoro-Ebah yace Tinubu ya mikawa hukumar INEC takardar karya a lokacin da zai yi takarar gwamnan jihar Legas wanda hakan ya sabawa dokoki.

Bola Tinubu a Jos
Asiwaju Bola Tinubu a Jos Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Lauyan yace ya bi ta hannun wani abokinsa, Mathew J. Kowals wanda ya yi masa bincike a Amurka, kuma ya gano akwai sabani a takardun Tinubu.

A cewarsa, Bola Tinubu ya fadawa jami’ar ta Chicago cewa a 1954 aka haife shi, amma da ya tashi cike takardar takarar shugaban kasa, sai yace 1952.

Lauyan yana ikirari akwai bambancin tambari da sa hannu tsakanin satifiket din da ya samu ta hannun jami’ar da kuma wanda shi Tinubu ya gabatar.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyoyi Sun Yi Gangami a Wata Jihar Arewa, Sun Yi Alkawarin Kawowa Tinubu Kuri'u Miliyan 4

Rahoton yace akwai ‘yan alamun tambaya a kan makarantun sakandaren da tsohon gwamnan na jihar Legas yake ikirarin ya halarta a shekarun baya.

The Cable tace karan su na gaban Mai shari’a Emmanuel Iyanna, kuma har zuwa lokacin da ake tattara rahoton nan, ba a sa ranar shari’ar ba tukun.

Tinubu bai taba aiki a Deloitte ba

Ku na da labari shiga takara ta sa an gano akwai ta-cewa a game da silar arzikin Bola Tinubu, an shiga bincike kan kamfanin da yace ya yi aiki tun a 1990s.

Baya ga bayanan da suka fito daga kamfanin Deloitte a Amurka, ana zargin ‘Dan takaran na APC da yi wa INEC karyar satifiket kafin shiga zaben 1999.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng