Gwamnatin Buhari ta Tsaida Lokacin da Za a Daina Saida Fetur da Araha a Najeriya

Gwamnatin Buhari ta Tsaida Lokacin da Za a Daina Saida Fetur da Araha a Najeriya

  • Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki ta kasa tace akwai shirin janye tallafin man fetur
  • Zainab Ahmed tace daga Mayun 2023, gwamnatin tarayya ba tayi tanadin cigaba da biyan tallafi ba
  • Ministar tayi wannan bayani a taron NESG, tace biyan kudin yana ci wa gwamnati tuwo a kwarya

Abuja - Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed, tace gwamnatin tarayya za ta daina biyan tallafin man fetur a shekarar 2023.

Vanguard ta rahoto Zainab Ahmed tana cewa daga Yunin 2023, gwamnatin tarayya ba za ta cigaba da kashe kudi saboda a saukake farashin man fetur ba.

Ministar tarayyar ta koro wannan bayani ne a wajen taron NESC ranar Talata a garin Abuja. Gwamnati ta dai kafe a kan maganar yin watsi da wannan tsari.

Ahmed tace janye tallafin yana cikin tsare-tsaren gwamnati a kasafin kudin shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Gaggawa Mai Sa Asara, Tsohon Shugaban Amurka Donal Trump Ya kaddamar da Takarar Shugaban Kasa

Inda gizo ke sakar

Kamar yadda This Day ta fada, Ministar tace babbar kalubalen da gwamnati za ta fuskanta shi ne yadda za a bi wajen janye wannan tallafi gaba daya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ministar tattali
Yemi Osinbajo da Ministar tattalin arziki a taro Hoto: @FinMinNigeria
Asali: Twitter

“Dole mu zauna da jama’a. Mun fara yin zama da jihohi da sauran mutane kafin a amince da hakan a tsarin tattalin arzikin kasa.
Dole ne mu bi shi a hankali, mu na sanar da mutanen Najeriya irin makudan kudin da ake batarwa wajen biyan tallafin fetur.
Sannan kuma akwai bukatarmu wayar da kansu a game da abubuwan da muka gaza yi saboda ana daukar nauyin tallafin.”

- Zainab Ahmed

Kudin da ake biya ya yi yawa

A cewar Ministar, biyan wadannan makudan kudi ya sa kasar a matsin lambar tattalin arziki, tace ta kai bashi ake karbowa domin a iya biyan kudi.

Kara karanta wannan

Fetur Zai Iya Haura N400, Gwamnoni Sun Bada Shawarar Gaggauta Janye Tallafi

Tsakanin Junairu zuwa Agustan shekarar bana, gwamnatin Muhammadu Buhari ta batar da fiye da Naira Tiriliyan 2.5 a wajen biyan tallafin man fetur.

NAN tace tsakanin Junairu da Yunin 2023, gwamnatin tarayya tayi tanadin Naira tiriliyan 3.3 da za a kashe saboda ‘yan kasa su saye litar mai da araha.

A cire tallafi - Gwamnoni

Kuna da labari shawarar da Gwamnoni suka ba Muhammadu Buhari a wajen taron NESG a birnin tarayya Abuja ita ce a daina biyan tallafin man fetur.

Malam Nasir El-Rufai yace duka Gwamnoni, da jami’an gwamnatin tarayya da sauran manyan kasa sun yarda ayi fatali da wannan tsari tun 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel