Gwamnatin Buhari ta Tsaida Lokacin da Za a Daina Saida Fetur da Araha a Najeriya
- Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki ta kasa tace akwai shirin janye tallafin man fetur
- Zainab Ahmed tace daga Mayun 2023, gwamnatin tarayya ba tayi tanadin cigaba da biyan tallafi ba
- Ministar tayi wannan bayani a taron NESG, tace biyan kudin yana ci wa gwamnati tuwo a kwarya
Abuja - Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed, tace gwamnatin tarayya za ta daina biyan tallafin man fetur a shekarar 2023.
Vanguard ta rahoto Zainab Ahmed tana cewa daga Yunin 2023, gwamnatin tarayya ba za ta cigaba da kashe kudi saboda a saukake farashin man fetur ba.
Ministar tarayyar ta koro wannan bayani ne a wajen taron NESC ranar Talata a garin Abuja. Gwamnati ta dai kafe a kan maganar yin watsi da wannan tsari.
Ahmed tace janye tallafin yana cikin tsare-tsaren gwamnati a kasafin kudin shekara mai zuwa.
Inda gizo ke sakar
Kamar yadda This Day ta fada, Ministar tace babbar kalubalen da gwamnati za ta fuskanta shi ne yadda za a bi wajen janye wannan tallafi gaba daya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Dole mu zauna da jama’a. Mun fara yin zama da jihohi da sauran mutane kafin a amince da hakan a tsarin tattalin arzikin kasa.
Dole ne mu bi shi a hankali, mu na sanar da mutanen Najeriya irin makudan kudin da ake batarwa wajen biyan tallafin fetur.
Sannan kuma akwai bukatarmu wayar da kansu a game da abubuwan da muka gaza yi saboda ana daukar nauyin tallafin.”
- Zainab Ahmed
Kudin da ake biya ya yi yawa
A cewar Ministar, biyan wadannan makudan kudi ya sa kasar a matsin lambar tattalin arziki, tace ta kai bashi ake karbowa domin a iya biyan kudi.
Tsakanin Junairu zuwa Agustan shekarar bana, gwamnatin Muhammadu Buhari ta batar da fiye da Naira Tiriliyan 2.5 a wajen biyan tallafin man fetur.
NAN tace tsakanin Junairu da Yunin 2023, gwamnatin tarayya tayi tanadin Naira tiriliyan 3.3 da za a kashe saboda ‘yan kasa su saye litar mai da araha.
A cire tallafi - Gwamnoni
Kuna da labari shawarar da Gwamnoni suka ba Muhammadu Buhari a wajen taron NESG a birnin tarayya Abuja ita ce a daina biyan tallafin man fetur.
Malam Nasir El-Rufai yace duka Gwamnoni, da jami’an gwamnatin tarayya da sauran manyan kasa sun yarda ayi fatali da wannan tsari tun 2021.
Asali: Legit.ng