‘Dan Majalisa Ya Yanke Jiki ya Fadi Ana Tsaka da Ralin Tinubu, Yace ga Garinku
- ’Dan majalisa mai wakiltar mazabar Mushin II dake jihar Legas ya yanke jiki ya fadi tare da rasa ransa
- Kamar yadda aka fi saninsa da Omititi a siyasance, yana daga cikin ‘yan siyasan da suka dira Jos wurin kaddamar da kamfen din Tinubu
- ‘Dan jam’iyyar APC din ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da zagayen a garin Jos inda kuma yace ga garinku bayan nan babu dadewa
Jos, Plateau - Honarabul Sobur Olayiwola Olawale, ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Mushin II a majalisar jihar Legas, ya rasu, Daily Trust ta rahoto.
An fi sanin shi da Omititi a bangaren siyasa, Olawale yana daga cikin ‘yan siyasan da suka dira garin Jos a jihar Filato domin kaddamar da yakin neman zaben Asiwaju Bola Tinubu a yau Talata.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mamacin ya yanke jiki ya fadi a yayin da ake zagayen kuma ya rasa ransa bayan nan.
Wata majiya tace ya yanke jiki ya fadi a filin jirgin sama kuma duk kokarin da aka yi na ganin ya farfado ya gagara.
Sai dai wani jigon APC wanda ya bukaci a boye sunansa ya sanarwa Daily Trust cewa sun yi kwanakin karshen mako tare da Olawale.
“Mun hadu a gidan Sanata Ganiyu Olanrewaju Solomon a ranar Lahadi kuma mun gaisa. Lafiya kalau muka gan shi. Babu ko tsammani, wannan hawan jini ne. Duk abinda zai kawo masa mutuwa yanzu abun tsoro ne.”
- Yace.
Majalisar jihar Legas ta fitar da takarda
A takardar da Honarabul Setonji David, Shugaban kwamitin yada labarai da tsaro na majalisar jihar Legas ya fitar, ya kwatanta lamarin da babbar asara, Vanguard ta rahoto.
Zaben 2023: Tinubu Ya Nuna Bajintarsa Ta Rawar Da Ba A Saba Gani Ba Yayin Da APC Ta Kaddamar Da Kamfen A Filato
“Cike da tsananin takaici da zuciya cike da rauni muke sanar da mutuwar abokin aikinmu, Honarabul Abdulsobur Olayiwola Olawale wanda aka fi sani da Omititi dake wakiltar mazabar Mushin ta 2 a majalisar jihar Legas.
“Har zuwa mutuwarsa, shi ne shugaban kwamitin kananan hukumomi kuma karo na biyu kenan da yake majalisar. Ya bar mu farat daya kuma ya saka mu jimami.
“Wannan mutuwar ta dake mu ba kadan ba. Zamu yi rashin shi fiye da yadda kalamai zasu bayyana. Muna kira gareku da ku yi masa addu’a da iyalansa a wannan lokacin. Mun gode.”
Asali: Legit.ng