Zan Nemi a Yafewa Najeriya Bashi Idan Na Zama Shugaba Kasa, Inji Atiku
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana shirinsa na habaka tattalin arzikin Najeriya
- Atiku ya ce zai nemawa Najeriya afuwar bashi daga kasashen waje da suke bin kasar kudade masu yawan gaske
- Najeriya na cikin rikicin tattalin arziki, ya zuwa yanzu bashin da ake bin kasar ya saka 'yan Najeriya cikin rudani
Jihar Legas - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce zai nemi a yafewa Najeriya bashin da ke kanta na kasashen waje idan ya gaji Buhari a 2023.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne a jihar Legas yayin da yake magana kan shirinsa na farfado tattalin arzikin Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa, shirinsa na mai da bangarori da dama hannun 'yan kasuwa zai samarwa 'yan Najeriya aikin yi.
Atiku ya yi wannan batu ne a wani taron tsoffin daliban makarantar kasuwanci ta Legas da aka gudanar na shekarar 2022, Punch ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake magana game da halin rikicin tattalin arziki da kasar ke fuskanta a yanzu, Atiku ya ba da misali da nasarorin da PDP ta samu tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007 sadda yake mataimakin shugaban kasa.
Mun yi a baya, yanzu ma za mu yi
A cewarsa, a wancan lokacin, gwamnatin PDP ta yi nasarar nemawa Najeriya afuwar bashin da ake binta, kana gwamnati ta habaka tattalin arzikin kasar cikin kankanin lokaci ta hanyar hada kai da kamfanoni masu zaman kansu.
A kalamansa:
"Idan ana magana game da bashin kasar waje, mun yi a baya, zan nemi wadanda suke bin bashin sannan na roki su yafe ko kuma su soke shi kamar yadda muka yi a baya.
"Game da bashin cikin gida, idan muka inganta tattalin arziki, za mu ke cin bashi kadan, mu kuma samar da hanyar biya ba tare da takura ba."
Ya kuma fadakar da jama'ar da suka halarci zaman kan lamuran da suka shafi tattalin arzikin kasa, tallafin man fetur, hada-hadar kudade, batun bashi da makamashi, Tribune Online ta ruwaito.
Hakazalika, Atiku ya tabo batun da ya shafi harkar man fetur da iskar gas a taron da manyan masu ruwa da tsaki da 'yan kasuwa suka halarta.
Shin akwai yiwuwar a yafewa Najeriya bashi?
Legit.ng Hausa ta tattauna da wani masanin tattalin arziki kuma malamin jami'a a Gombe, Muhammadu Shamsudden Sani, wanda ya yi tsokaci kan yiwuwar yafe bashin Najeriya.
Ya shaida cewa:
"Abin da Najeriya ke bukata farko a yanzu shine tabbatar da an habaka hanyoyin shigowar kudae da kuma rage kashe kudade kan ayyukan da ba sa dawo da riba.
"Za a iya yafe bashin Najeriya idan aka bi yadda lamarin yake, amma zai ba da wahala matuka, don haka baya ga neman yafe bashi, akwai bukatar tunanin hanyoyin samun karin kudin shiga.
"Ya faru a baya, ya faru da kasashe da yawa, muna fatan a yi hakan yanzu."
Atiku waliyyi ne kan Tinubu da Peter Obi, inji jigon PDP
Wani jigon PDP, Reno Omokri ya kwatanta tarihin rayuwar Atiku da sauran 'yan takarar shugaban kasa, musamman na jam'iyyun Labour da APC.
Omokri ya ce, Atiku na da tsafta idan aka kwantanta shi da Tinubu ko Peter, tare da cewa ba a taba tuhumar Atiku da laifi ba a Najeriya.
Ya kuma yi tsokaci game tuhumar da ake yiwa Tinubu a Amurka da kuma yadda aka ambaci Peter Obi a takardun Pandora.
Asali: Legit.ng