2023: Bola Tinubu Ya Yi Subutar Baki, Yace Allah Ya Albarkaci PD....APC, Bidiyo Ya Fito

2023: Bola Tinubu Ya Yi Subutar Baki, Yace Allah Ya Albarkaci PD....APC, Bidiyo Ya Fito

  • A ranar farko ta kamfe ɗinsa, Bola Ahmed Tinubu ya yi subutar baki yayin da yake kokarin cewa Allah ya albarkaci APC a Jos
  • Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna yadda Tinubu yace Allah ya albarkaci PD... Sai kuma ya gyara
  • A ranar Talata, 15 ga watan Nuwamba, 2022, Tinubu ya kaddamar da fara yakin neman zaɓe a Jos, jihar Filato

Jos, Plateau - Ɗan takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya karkashin inuwar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi subutar harshe yayin da yake jawabi a wurin buɗe kamfe dinsa a jihar Filato.

Jaridar The Cable tace gangamin taron ya gudana ne a a babban filin Rwang Pam township stadium, da ke Jos, babban birnin jihar Filato ranar Talata.

Kara karanta wannan

A yi dai mu gani: Tinubu ya tara jama'a, ya yiwa Atiku da Peter tonon silili a Jos

Bola Ahmed Tinubu.
2023: Bola Tinubu Ya Yi Subutar Baki, Yace Allah Ya Albarkaci PD....APC, Bidiyo Ya Fito Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Yayin da yake ƙarƙare jawabinsa a wurin taron, Bola Tinubu yace, "Allah ya albarkaci PD..." sai kuma ya yi sauran gyara wa zuwa, "Allah ga albarkaci APC."

"Allah ya Albarkaci PD... APC, Allah ya Albarkaci APC APC, Allah ya albarkaci APC. Mu zamu samu nasara, Allah ya muku Albarka," inji shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli Bidiyon anan

Dole mu haɗa kai mu yi aiki tare - Adamu

A nasa jawabin, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, yace akwai bukatar jam'iyyar ta dage ta yi aiki tukuru domin lashe babban zaɓen 2023.

Adamu yace:

"Damar jam'iyya mai mulki na ci gaba da jan zarenta a Ofis bai gushe ba, A ko da yaushe ina jaddada yin aiki tukuru, na fahimci muna bukatar mu haɗa kai wuri ɗaya mu yi aiki tare.

Kara karanta wannan

Tinubu: Zan Kora Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Koma Mahaifarsa a 2023, Ya Faɗi Suna

"Nasarorin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya samu sun kere na waɗanda ya gada. A shekaru Bakwai da ya shafe a Ofis, Titunan mu, Filayen jiragenmu sun sauya."

'Yan adawa basu da bakin magana - Lawam

Haka nan a nasa jawabin, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, yace jam'iyyun adawa da ke kokarin gogayya da APC ba su da bakin magana.

"Mai girma shugaban ƙasa kai gwarzo ne a ayyukan raya ƙasa a Najeriya, shugaban mu mai jiran gado zai ɗora daga nan, masu son gogayya damu basu da abin magana. Abu kaɗan PDP ta yi duk da arzikin data samu."
"A tsawon shekara 16 jihar Filato bata san menene zaman lafiya ba amma daga 2015 da Lalonga ya hau Mulki, jihar Filato ta samu zaman lafiya."

A wani labarin Ɗan majalisar dokokin jihar Legas, wanda ya yanki jiki ya faɗi ana tsaka da gangamin Bola Tinubu a Jos ya kwanta dama

Kara karanta wannan

Ali Nuhu, da Wasu Jaruman Kannywood da Nollywood Sun Halarci Kamfen Tinubu, Sun Bada Nishaɗi

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Mushin II a majalisar dokokin jihar Legas, Honorabul Sobur Olayiwola, na daga cikin waɗanda suka halarci buɗe kamfen APC a Jos.

An tattaro cewa ɗan siyasan ya faɗi yayin da ake zagaye kuma rai ya yi halinsa bayan wasu yan mintuna da faruwar haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262