Ali Nuhu, Jide Kosoko da Wasu Fitattun Jaruman Kannywood da Nollywood Sun Halarci Gangamin Tinubu
- Shahararrun jaruman Kannywood da Nollywood sun halarci gangamin yakin Neman zaɓen Bola Tinubu a Jos
- Ali Nuhu ya yi jawabi a madadin takwarorinsa na Kannywood, inda yace zasu yi duk me yuwuwa na haɗa wa Tinubu masu zabe
- Jaruman dai sun taka rawa bayan sanya wakoki daban-daban domin jaddada goyon bayansu
Jos, Plateau - Wasu jaruman fina-fainai daga masana'antar Kannywood da Nollywood sun halarci ganganin kamfen Bola Tinubu da ke gudana yanzu haka a Jos, babban birnin jihar Filato.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa wasu daga cikin Shahararrun jaruman da aka hanga a wurin sun haɗa da, Ali Nuhu, Jide Kosoko, Gentle Jack, Sani Mu’azu da Foluke Daramola.
Sauran sun haɗa da, Zack Orji, Said Balogun, Taiwo Hassan, Bimbo Akintola da dai sauransu daga Masana'antun Kannywood ta arewa da Nollywood ta kudancin ƙasa.
Ali Nuhu, wanda ya yi jawabi a madadin abokan sana'arsa na Kannywood, ya bukaci 'yan Najeriya su mara wa Tinubu/Shettima baya a zaɓe mai zuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kuma roki dukkanin wani ɗan Najeriya da har yanzun bai karɓi Katin zabensa ba ya gaggauta zuwa ya karɓo domin ta haka ne kaɗai zai samu damar kaɗa kuri'a.
Sarki Ali yace zasu yi duk mai yuwuwa wajen haɗa kan mambobi da masoyansu a bayan tikitin Tinubu/Shettima.
"Na zo nan tare da wasu abokan sana'ata kuma mun kawo kanmu nan ne domin muna tare da Tinubu," Inji Sarki Ali Nuhu.
A nasa taƙaitaccen jawabin, Jide Kosoko, yace sun halarci gangamin Jos ne domin su nuna wa Tinubu ana tare, wanda a cewarsa yana da kwarewar magance kalubalen ƙasar nan.
Kosoko ya bayyana cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da zai iya a dukkanin muƙaman da ya riƙe a baya.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Jaruman sun taka rawa yayin da aka sa waƙoƙi daban-daban domin jaddada matsayarsu ga ɗan takarar jam'iyyar APC.
Buhari Ya Ɗaga Darajar Najeriya Har Ta Wuce Manyan Kasashen da Suka Cigaba, Bello
A wani labarin kuma A wurin gangamin kamfen Tinubu, Yahaya Bello ya sha alwashin tattara wa Tinubu matasan Najeriya a zaɓen 2023
Da yake nasa jawabin, gwamnan jihar Kogi, Ko'odinetan matasa, yace mulkin APC tun zuwam Buhari ya ɗaga daraja da ƙimar Najeriya a idom duniya
Gwamnan yace sakamakon ayyukan raya ƙasa da shugaba Buhari ya aiwatar, Najeriya ta kere ƙasashe da dama ciki harda waɗanda suka cigaba.
Asali: Legit.ng