Jerin Gwamnonin PDP da Suka Gindaya Sharuda Kafin Su Goyi Bayan Atiku Abubakar
- Jam’iyyar PDP ta gamu da rigingimun cikin gida iri-iri tun da Atiku Abubakar ya samu tiktin takara
- Akwai wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP musamman Gwamnonin jihohi da ke yakar ‘dan takaran na 2023
- Gwamnonin sun gindaya sharudan da sai an cika sannan za su bada gudumuwa a zaben shugaban kasa
Nigeria - Jam’iyyar hammaya ta PDP tana fama da rikici daga cikin gidanta yayin da ake shiryawa babban zabe a farkon shekarar badi.
Akwai gwamnonin jam’iyyar da ke rigima da Dr. Iyorchia Ayu, kuma sun ce ba za su goyi bayan Atiku Abubakar sai an cika masu sharuda.
Legit.ng ta kawo wadannan Gwamnoni da ake dauki babu dadi da ita:
1. Samuel Ortom
2. Nyesom Wike
3. Seyi Makinde
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Samuel Ortom
Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom yana cikin manyan masu yakar Atiku Abubakar, har ta kai ya kira masu goyon bayan ‘dan takaran da makiyin jiharsa.
Tun kwanaki Mai girma Samuel Ortom yace ba zai taba goyon bayan Atiku a 2023 har sai ‘dan takaran ya nemi afuwarsa kan abin da ya faru tsakaninsu.
Nyesom Wike
Nyesom Wike bai ji dadin yadda zaben tsaida gwanin ta kaya a jam’iyyar PDP ba. Gwamnan na Ribas ya zo bayan Atiku Abubakar wajen samun tikiti.
Gwamnan ya yi alkawarin ba zai taya Atiku yakin neman zaben shugaban kasa ba saboda zargin cewa ‘dan takaran bai dauki mutanen Ribas da daraja ba.
Seyi Makinde
Shi ma Seyi Makinde yana cikin gwamnonin da ke tare da tafiyar Nyesom Wike, yace dole sai an yi gyara a jam’iyyar PDP muddin ana so su taimaki Atiku.
Kwanakin baya aka ji mataimakinsa ya halarci taron Afenifere, har ya shaidawa Duniya cewa Gwamna Makinde yana goyon bayan Bola Tinubu a 2023.
Bala Mohammed
Legit.ng Hausa ta kara da Mai girma Bala Mohammed na Bauchi a jerin gwamnonin da suka yi turjiya wajen goyon bayan Atiku saboda sabani tsakaninsu.
A wata wasika da ya aikawa shugaban PDP na kasa, Gwamna Bala Mohammed ya yi barazanar cire hannunsa, yana mai neman ‘dan takaran ya roki afuwa.
Gwamnoni na sata da wayau - Kwankwaso
An rahoto tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso yace da sunan kudin tsaro Gwamnoni suke tafka katuwar sata cikin ruwan sanyi a Kasar nan.
‘Dan takaran Shugaban kasan na jam'iyyar NNPP ya sha alwashin dakatar da biyan wadannan kudi muddin ya yi nasarar karbe shugabancin Najeriya a badi.
Asali: Legit.ng