Rigingimun PDP: Nan Ba Da Jimawa ba Atiku Da Wike Zasu Shirya, Saraki

Rigingimun PDP: Nan Ba Da Jimawa ba Atiku Da Wike Zasu Shirya, Saraki

  • Tsohon gwamnan Kwara, Bukola Saraki, yace nan ba da jimawa ba jam'iyyar PDP zata ba yan Najeriya mamaki
  • Tsohon shugaban majalisar dattawa yace zasu warware saɓanin da ya haɗa Wike da Atiku faɗa a jam'iyyar PDP
  • Saraki ya tuna da kyawawan alheran mahaifinsa wanda aka gudanar da Addu'ar cikarsa shekara 10 da rasuwa

Kwara - Taohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki, yace nan ba da jima wa ba rigingimun da suka addabi jam'iyyar PDP zasu zama tarihi.

Vanguard ta rahoto Saraki na cewa nan da wani ɗan lokaci za'a sulhunta da warware saɓanin dake tsakanin ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsagin Gwamna Wike na Ribas watau G5.

Bukola Saraki.
Rigingimun PDP: Nan Ba Da Jimawa ba Atiku Da Wike Zasu Shirya, Saraki Hoto: Dr. Abubakar Bukola Saraki
Asali: Facebook

Saraki ya yi wannan furucin ne a Ilorin ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai a wurin Addu'ar cikar mahaifinsa, ɗan siyasa tun a jamhuriya ta farko, Olusola Saraki, shekara 10 da rasuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Halaka Matar Shugaban Ƙaramar Hukuma a Jihar Arewa

Saraki, tsohon gwamnan jihar Kwara, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Jam'iyyar PDP zata ba 'yan Najeriya mamaki, zamu haɗa kai a inuwa ɗaya mu yi aike tare domin goben Najeriya ta yi kyau."
"Hakan zata faru ne saboda ba abinda ke zuciyoyin mu sai tunanin matsalolin da kasar nan ke fama da su da kuma hanyoyin warware su. Ku duba yadda talauci ya zama ruwan dare, gwamnati ba ta yin komai."
"Zamu sa bukatun yan Najeriya a gaba domin burinsu PDP ta koma kan madafun iko. Ɗan karamin saɓanin dake tsakanin Atiku da Wike zamu warware shi kuma a ƙarshe ko a wane tsagi kake, fatanmu Najeriya ta gyaru."

Daily Trust tace yayin da yake tuna wasu lokuta a rayuwar marigayi mahaifinsa, Saraki ya ƙara da cewa:

"Wani lokaci ya bani shawarin na shiga siyasa, ba abu ne mai sauki ba, yaƙi ne amma na zulle. Amma a yau ina ganin babban ci gaba a rayuwa shi ne ka ga mutane sun cigaba."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Ta'adda Sun Aike da Sako, Sun Yi Barazanar Tilasta Wa Wani Gwamna Ya Yi Murabus

"Abun da ya rage mana mu 'ya'yansa shi ne mu ɗora daga inda ya tsaya mu tabbata rayuwar mutane ta inganta kuma mu tsaya kan gaskiya."

Sanatan PDP daga Enugu ya kara yaba wa Tinuhu

A wani labarin kuma Sanata Nnamani Ya sake fitowa fili ya yi kalaman yabo ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, Bola Ahmed Tinubu

Sanatan, wanda ya shiga jerin tawagar kamfen Tinubu na farko, yace lokacin da ɗan takarar ke gwamnan Legas ya taka muhimmiyar rawa a ɓangaren shari'a.

Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan Nnamani ya bukaci Inyamurai su daina faɗa da yarbawa, su fara duba yuwuwar kafa gwamnatin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262