Atiku a Tsaftace Yake Sabanin ’Yan Takara Irin Su Tinubu da Obi, Inji Reno Omokri
- An zargi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu da hannu a harkallar miyagun kwayoyi a kasar Amurka
- An zargi Peter Obi kuma da hannu a rashawa a takardun Pandora da aka fitar a shekarar 2021 tare da wasu shugabannin duniya
- Reno Omokri ya yi duba da wannan lamari, ya ce dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar waliyyi ne a kan su Tinubu da Obi
Najeriya - Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan, Reno Omokri ya bayyana cewa, dan takarar shugaban kasa na PDP a tsaftace yake idan ana maganar rashawa sabanin Peter Obi da Bola Tinubu.
Omokri ya bayyana hakan ne a wani rubutun da ya yada a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, inda yace 'yan takarar shugaban kasa na APC; Bola Tinubu da na LP; Peter Obi duk an taba tuhumarsu da batun rashawa.
Tsohon hadimin na Jonathan ya yi wannan tsokaci ne a martaninsa ga wasu takardu da ke yawo masu tuhumar Tinubu da harkallar miyagun kwayoyi daga Amurka.
Omokri ya tabo batun Peter Obi
A bangare guda, Omokri ya tabo Petero Obi, inda yace an taba ambato Peter Obi a jerin sunayen wadanda ake zargi da rashawa a takardun Pandora da aka saki a shekarar 2021.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A rubutun nasa, Omokri cewa ya yi:
"Atiku Abubakar shi ne dan siyasan da aka fi bincika a Najeriya, amma ba a taba kama shi da wani abu ba. Shi ba abin zargi bane a kudaden miyagun kwayoyi, kamar Tinubu, ko kuma aka ambace shi a takardun Pandora saboda rashawa, kamar Peter Obi."
Tinubu dai ya fuskanci maganganu masu tada hankali daga jam'iyyun adawa tun bayan da aka fitar da wasu takardun kotun Illinois a kasar Amurka da ke zargin hannun Tinubu a harkallar miyagun kwayoyi na $460,000.
Sai dai, kakakin APC, Festus Kayemo, ya kare Tinubu da cewa, kudaden da ake zargin ba komai bane illa haraji sabanin jita-jitar da ke yadawa cewa na harkallar kwaya ne.
Ba zan tafi kasar waje a duba lafiyata ba, inji Kwankwaso
Shi kuwa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP cewa, ya yi, ba zai zama irin shugabannin Najeriya ba, domin zai dakata da batun zuwa kasar waje duba lafiya.
Rabiu Musa Kwankwaso ya ci alwashin gyara fannin lafiya tare da habaka kayan aiki masu kyau don kawo mafita ga fannin a Najeriya.
'Yan siyasa na ci gaba da tallata kansu gabanin zaben 2023 mai zuwa.
Asali: Legit.ng