2023: Peter Obi Babbar Barazana Ce Ga Nasarar PDP, Gwamnan Anambra
- Gwamnan Anambra ya ayyana cikakken goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APGA, Peter Umeadi
- Soludo, wanda ya ɗare kujerar gwamna a inuwar APGA yace LP da Peter Obi barazana ce mai girma ga PDP ba wai jam'iyyarsa ba
- Gwamnan ya jaddada cewa magoya bayan Obi ba zasu iya dakile shirin da APGA ta yi a zaɓen 2023 ba
Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya ayyana cikakken goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APGA, Farfesa Peter Umeadi.
Gwamna Soludo yace ɗan takarar Labour Party (LP), Peter Obi, da magoya bayansa da suka shahara da 'Obidients' ba wata barazana bace ga jam'iyyar APGA, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Yace tafiyar Obidients tamkar saran ƙafa ne ga babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, The Nation ta ruwaito.
A wata sanarwa da mai bashi shawara kan harkokin siyasa, Dr Alex Obiogbolu, ya fitar ranar Lahadi, gwamnan jihar Anambra ya yi ikirarin cewa har yau APGA ce jam'iyya ta uku mafi girma a Najeriya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
PDP bata yi wa kudu maso gabas adalci ba - Soludo
Soludo, wanda ya yi imanin cewa babbar jam'iyyar adawa ta zalunci yankin kudu maso gabas ta hanyar kai tikitin takara arewa, yace goya wa wata jam'iyya ka iya dusashe damar APGA na lashe zaɓen 2023 mai zuwa.
Sanarwan ta ce:
"Har yanzu APGA ce jam'iyyar siyasa ta uku mafi girma a Najeriya idan aka yi la'akari da kujerun siyasar da take da su."
"Jam'iyyar APGA na da gwamnan jiha ɗaya, mambobin majalisar tarayya da kuma mambobi a majalisar dokokin jihohi. APGA ba ta kallon tafiyar Peter Obi a matsayin wata barazana ga kokarin cimma kudirinta a 2023."
"Jam'iyyar LP da tafiyar 'yan Obidients na sare ƙafar PDP ne. Saboda haka sun zama ƙalubale, barazana ga jam'iyyar PDP, ba abinda ya shafi APGA."
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Charles Soludo ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra karkashin inuwar jam'iyyar APGA.
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC na gab da buɗe kamfen a Filato, Hadimin gwamnan Kwara ya yi murabus daga mukaminsa
An tattaro cewa rigingumu sun yi wa jam'iyyar APC reshen jihar Katutu kuma ba wannan ne karon farko da na hannun daman gwamna AbdulRazaq ya aje aiki ba.
Sai dai a cewarsa mashawarcin gwamna na musamman kan harkokin wasanni da matasa, Ibrahim Attahiru, ya yi murabus ne bisa dalilai na ƙashin kansa.
Asali: Legit.ng