Gwamna Buni Ya Rantsar da Shugaban Ma'aikata da Shugabannin Kananan Hukumomi a Yobe

Gwamna Buni Ya Rantsar da Shugaban Ma'aikata da Shugabannin Kananan Hukumomi a Yobe

  • Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya rantsar da sabon shugaban ma'aikatan jiharsa bayan shafe lokaci a matsayin na riko
  • Bayan haka, Buni ya rantsar da Kantomomin da zasu kula da kananan hukumomi 17 da ke faɗin jiharsa
  • Yace naɗinsu ya zo ne a lokacin da wa'adin waɗanda mutane suka zaɓa ya zo ƙarshe, ya roki su yi aikin da ya dace

Yobe - Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya rantsar da Alhaji Garba Bilal a matsayin shugaban ma'aikata da kuma shugabannin ƙananan hukumomi 17 na rikon kwarya.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Bilal ya kasance a matsayin muƙaddashin shugaban ma'aikatan Yobe tun watan Afrilu, 2022.

Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni.
Gwamna Buni Ya Rantsar da Shugaban Ma'aikata da Shugabannin Kananan Hukumomi a Yobe Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

Game da kantomomi, Gwamna Buni yace an naɗa su ne sakamakon ƙarewar wa'adin zaɓaɓɓun Ciyamomin kananan hukumomin jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC Ta Lallasa Jam'iyyu 12, Ta Lashe Zaben Ciyamomi 25 a Jihar Arewa

Haka nan gwamnan yace ya zakulo su ne bisa la'akari da zagewarsu a wurin aiki, biyayya, kwarewa da burinsu na yi wa al'umma aiki tun daga tushe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buni ya kuma buƙaci sabbin Ciyamomin da su maida hankalin wajen lalubo hanyar karuwar kuɗaɗen shiga a yankunansu domin ta haka ne kaɗai gwamnati zata samu kuɗaɗen tafiyar da ɓangaren Ilimi, Noma, Lafiya da samar da ruwa.

Bugu da ƙari ya tabbatarwa Kantomomin cewa gwamnatinsa zata taimaka musu bakin gwarwardon hali domin su inaganta rayuwar talawakan yankunansu.

Jerin sunayen Waɗan da Buni ya naɗa

Waɗanda gwamnan ya naɗa a matsayin Kantomomi da kuma yankin da zasu yi aiki:

1. Alh Ibrahim Babagana – Bade

2. Lawan Bukar – Bursari

3. Bukar Adamu – Damaturu

4. Hajiya Halima Kyari Joda – Fika

5. Baba Goni Mustapha – Fune

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wasu Ɗalibai Biyu Na Wata Jami'a a Najeriya Sun Mutu a Ɗakin Kwana

6. Ali Kolo Kachalla – Gaidam

7. Dala Mala – Gujba

8. Dayyabu Ilu – Gulani

9. Abdullahi Ahmed Garba – Jakusko

10. Lawan Alhaji Gana – Karasuwa

11. Bukar Abubukar – Machina

12. Alh Salisu Yerima – Nangere

13. Alh Modu Kachalla – Nguru

14. Alh Salisu Muktari – Potiskum

15. Mohammed Lamido Musa – Tarmuwa

16. Dauda Bukar – Yunusari

17. Alh Waziri Ibrahim – Yusufari.

A wani labarin kuma tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega da Hakeem Baba Ahmed, sun ayyana goyon bayan ga ɗan takarar PRP a 2023.

Jega yace waɗanda ke zuzuta cewa zaɓen shugaban kasan 2023 na mutum uku ne suna ba shi dariya, a cewaraa ba'a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare.

Yace Kola Abiola, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PRP, mutum ne ya cancanta fiye da kowa ya kafa gwmanati a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262