Rikicin PDP: Ban Rufe Kofar Sulhu Ba, Atiku Ya Bawa Wike Amsa

Rikicin PDP: Ban Rufe Kofar Sulhu Ba, Atiku Ya Bawa Wike Amsa

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya ce har yanzu kofa a bude ta ke don yin sulhu da bangaren Wike
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a matsayin martanin kan jawabin da Wike ya yi a Bauchi na cewa kofarsu a bude ta ke don tattaunawa
  • Wike da wasu gwamnoni 4 da ake kira G5 sun janye daga kwamitin takarar shugaban kasa na PDP ne kan cewa dole sai shugaban jam'iyyar Iyorchia Ayu ya yi murabus

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce bai rufe kofa ba don yin sulhu da mutanen bangaren Gwamna Nyesom Wike, Daily Trust ta rahoto.

Bangaren na Wike sun fita daga kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku ne kuma suka nemi Sanata Iyorchia Ayu ya yi murabus a matsayin shugaban jam'iyya na kasa saboda adalci da daidaito.

Kara karanta wannan

Karshen rikicin PDP: Wani tsohon shugaban kasa zai sulhunta Atiku da tawagar Wike

Atiku da Wike
Rikicin PDP: Ban Rufe Kofar Sulhu Ba, Atiku Ya Bawa Wike Amsa. Hoto: Naija News
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma, da ya ke magana a ranar Laraba a Bauchi, Wike, wanda shine jagoran gwamnonin da ke bore a PDP, yayin ziyarar da suka kaiwa takwararsu Bala Mohammed na Bauchi ya ce har yanzu a shirye suke suyi sulhu da shugabannin jam'iyyar.

Martanin Atiku

Da ya ke martani kan kalaman na Wike, tsohon mataimakin shugaban kasar ta bakin kakakinsa Paul Ibe ya ce ba a rufe kofan sulhu da wadanda ke ganin an zalunce su ba, Vanguard ta rahoto.

Ya ce:

"Dan takarar shugaban kasa na PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar na maraba da rahoton cewa Gwamnan Rivers Nyesom Wike da tawagarsa na fatan warware matsalolin da ke tsakaninsu da dan takarar na PDP.
"Atiku Abubakar ya bayyana kudirinsa na yin tattaunawa da za ta warware rikicin tare da share fage don samar da PDP kakarfa da hadin kai. Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce babu lokacin da ya taba rufe kofar sulhu da bangaren Wike.

Kara karanta wannan

'Ƙawancen' Buhari Da Tinubu Za Ta Wargaje A 2023, In Ji Atiku

"Ya yi kira ga duk wani jagora da magoya bayansu daga kowanne bangare su zama masu budaddiyar zuciya tare da goyon bayan warware rikicin."

Gwamnonin PDP Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu

Jam'iyyar PDP ta tsinduma cikin rikici tun bayan da Atiku Abubakar ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasa na zaben 2023.

Saboda tsadar rayuwa da wasu matsalolin, wasu yan kasar na goyon bayan jam'iyyar hamayyar ta kwace mulki daga APC a zaben da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164