Tinubu: Mun Samu Dabarar da Za Mu Bi Wajen Lahanta Kwankwaso a Arewa Inji PCC
Hon. Aminu Jaji ya kaddamar da kwamitinsa da zai yi wa Jam’iyyar APC aiki a jihohin Arewa maso yamma
‘Dan siyasar yace lokaci ya yi da ‘Yan Arewa maso yamma za su goyi bayan Bola Tinubu ya zama Shugaban kasa
Kwamitin neman takaran yace ba za su bari shiga takarar Rabiu Kwankwaso ta kawowa APC cikas a yankin ba
Abuja - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, yace ya gano dabarar karya Rabiu Musa Kwankwaso mai neman takara a NNPP.
This Day ta rahoto Aminu Jaji wanda shi ne shugaban kwamitin tattara jama’a a shiyyar Arewa maso yamma yana wannan jawabi a ranar Alhamis.
Hon. Aminu Jaji ya kaddamar da ‘yan kwamitinsa a garin Abuja, ya shaida masu cewa wanda mutanen Arewa maso yamma suka zaba ne zai ci zabe.
Shugaban wannan kwamiti yake cewa lokaci ya yi da al’ummar yankinsa za su mara baya ga Asiwaju Bola Tinubu ya karbi shugabancin Najeriya a 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kamata yanzu a bi bayan Tinubu - Jaji
Jaji yake cewa Bola Tinubu mai takara yanzu, ya ba Muhammadu Buhari hadin-kai a 2015 da 2019.
"Babban abin da za mu iya yi a 2023 shi ne sakawa Tinubu, wanda ya goyi bayan na mu ya zama shugaban kasa sau biyu.
Lokaci ya yi da za muyi irin abin da mutanen sauran bangarori suka yi wa ‘dan mu, ubanmu kuma abin koyin mu – Buhari.
Mutanen Kudu maso yammacin Najeriya sun kafe, sun mara masa baya komai runtsi.
Lokaci ya yi da za mu goyi bayan Asiwaju Bola Tinubu, amma da sharadi, zai taimakawa cigaban yankin Arewa musamman.”
Yadda za muyi wa Kwankwaso
Mataimakiyar sakariyar kwamitin, Dr. Talatu Nasir tace duk da ‘dan takaran jam’iyyar NNPP ya fito daga yankin, ba zai hana APC samun nasara ba.
Leadership ta rahoto Talatu Nasir tana cewa sun gano hanyar da za a bi wajen ganin Rabiu Musa Kwankwaso bai iya yin tasiri a zaben shugabancin kasar ba.
PCC zai cin ma wannan buri ta hanyar bi gida zuwa gida da rumfar zabe domin tallata Tinubu.
Zan farfado da tattali - Tinubu
A jiya ne aka samu rahoto Bola Tinubu ya zauna da mutane a jihar Nasarawa, a nan ya yi masu bayanin yadda gwamnatinsa za ta inganta tattalin arzikin Najeriya.
Bola Tinubu ya yi alkawarin kammala aikin Ajaokuta har kamfanin ya soma yin aiki a Najeriya. ‘Dan siyasar yace zai bunkasa harkar noma idan ya iya yin nasara.
Asali: Legit.ng