Ka Shiya Zama Shugaban Kasan Najeriya, Shugaban APC Ya Fadawa Bola Tinubu

Ka Shiya Zama Shugaban Kasan Najeriya, Shugaban APC Ya Fadawa Bola Tinubu

  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa ya bayyana kwarin gwiwarsa ga nasarar lashe zaben Bola Tinubu a zaben 2023 mai zuwa badi
  • Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci 'yan Najeriya da su natsu, su ba da kuri'unsu ga Bola Ahmad Tinubu a zaben mai zuwa
  • Jigon jam'iyyar APC ya ce, Bola Tinubu ne dan takarar shugaban kasan da ba zai wawuri kudin kasar nan ba idan ya zama shugaban kasa

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, sanata Abdullahi Adamu ya karawa dan takarar shugaban kasansu, Bola Ahmad Tinubu kwarin gwiwar lashe zaben 2023.

A ranar Alhamis 10 ga watan Nuwamba, Adamu ya shaidawa Tinubu cewa, yanzu kam ya shirya zama shugaban kasan Najeriya kawai, The Nation ta ruwaito.

Adamu, wanda ya bayyana hakan a wani taron jama'a da aka gudanar birnin Lafia na jihar Nasarawa, ya ce ya zuwa yanzu dai ya fara jin kamshin Tinubu ya gaji kujerar Buhari.

Kara karanta wannan

2023: Shettima ya caccaki Atiku da Obi, ya ce ba za su tsinanawa 'yan Najeriya komai ba

Ka shiya zama kan kujerar shugaban kasa, Adamu ga Tinubu
Ka shiya zama shugaban kasan Najeriya, shugaban APC ya fadawa Bola Tinubu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Buhari ya ce Tinubu zai gaje shi a 2023, inji Adamu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wata sanarwa aka fitar a Abuja ta hannun daraktan yada labaran APC, Bayo Onanuga, an naqalto Adamu na cewa:

"Idan ban da Allah, shugaba Buhari ne mafi iko a Najeriya a yau. Buhari ya fadi haka kuma zai zo ya wuce."

Ya kira Tinubu ya tashi tsaye a wurin taron tare da mutanen da suka halarta, daga nan ya ayyana cewa, Tinubu zai zama shugaban Najeriya na gaba.

Ya kuma shawarci 'yan Najeriya da su fito kwansu da kwarkwata su ba da kuri'unsu ga Tinubu a zaben 2023, PM News ta ruwaito.

Daga nan kuma ya bukaci Tinubu ya shirya kama aiki a matsayin shugaban kasa tare da shirya daukar nauyin da za a daura masa na shugabancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yayin da Yake Kasar Waje, Buhari Ya yi Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance

Wannan batu na Adamu dai ya jawo tafi da yabo tsakanin wadanda suka halarci taron a babban dakin taron gidan gwamnatin Nasarawa.

Daga karshe, Tinubu ya yi alkawarin taimakawa jihar Nasarawa ta fuskar masana'antu domin tabbatar da ci gaban jihar.

Tinubu ba zai saci kudin 'yan Najeriya ba

A bangare guda, jigon APC a jihar Zamfara ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali, Tinubu ba zai saci kudin 'yan Najeriya ba.

Yusuf Idris, wanda shine kakakin APC a jihar ya ce Tinubu ne ya cancanci gaje Buhari, kuma zai habaka tattalin arzikin kasar nan.

Hakazalikam Idris ya ce Tinubu zai mai da hankali kan hanyar da za ta kawo karshen matsalolin tsaron kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.