APC Ta Tanka Zargin da Ake Yi Wa Tinubu Na Harkar Kwayoyi a Kasar Amurka

APC Ta Tanka Zargin da Ake Yi Wa Tinubu Na Harkar Kwayoyi a Kasar Amurka

  • Mai magana da yawun bakin kwamitin neman zaben Tinubu/Shettima ya wanke Bola Tinubu daga zargi
  • Festus Keyamo yace zargin da ake jifan ‘dan takaran APC da shi na yin alaka da kwayoyi ba gaskiya ba ne
  • Ana jita-jita cewa kotu ta taba samun Tinubu da laifin harkar miyagun kwayoyi a lokacin da yake Amurka

Abuja - Festus Keyamo wanda shi ne Mai magana da yawun kwamitin takarar Tinubu/Shettima ya yi karin haske a zargin da ake yi wa Bola Tinubu.

A wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba a gidan talabijin Channels TV, Festus Keyamo yace zargin da ake jifar Bola Tinubu da shi ba gaskiya ba ne.

Keyamo ya maida martani ne biyo bayan wani labari da ‘yan adawa ke yadawa cewa wata kotu a kasar Amurka ta taba samun ‘dan takaran na su da laifi.

Kara karanta wannan

Yayin da Yake Kasar Waje, Buhari Ya yi Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance

A cewar Kakakin kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC, ba a taba maka Bola Tinubu a kotun Amurka, yace an yi shari’a ne da asusun bankinsa.

Ba a kai Tinubu kotu ba - Keyamo

"Ba za ta yiwu a same shi da laifi bai dan har ba Asiwaju aka yi kara ba, ko bai cikin wadanda aka yi shari’a da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zan kara maimaitawa a wani karo na bila-adadin, ka da in ta yin magana daya, ba ayi shari’ar nan da Tinubu ba.
Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu Hoto:@officialasiwajubat
Asali: Twitter
Akawun dinsa kurum aka yi kara a kotu, ba shi ba.
Akawun din banki ne da sunansa aka maka a kotu domin ayi shari’a, ta ya za a kama shi da laifi idan babu akawun?"

- Festus Keyamo

An yi shari'a a kan akawun 10

Kara karanta wannan

Abin ya fara yawa: Ni da Masoyana Na Fuskantar Hadari Daga APC - Atiku Ya Koka

Vanguard tace da aka tambayi Ministan tarayyan ko akawun nawa aka yi bincike a kai, sai yace goma ne a wasu bankuna uku na kasar ketaren.

Kamar yadda Keyamo ya fada, ba duka akawun din ba ne ke dauke da sunan Tinubu, akwai na mahaifiyarsa, amma sai ya dauki nauyin dangin na sa.

“Ya dauki nauyin dukansu saboda da sunan dangin Tinubu su ke. Akwai na mahaifiyarsa, akwai na kamfaninsa, akwai na ‘danuwansa.
A karshe kuma sai aka roke shi cewa ‘ka da ka kalubalance mu idan an gano cewa an yi kuskure wajen rufe akawun din tun da farko.”

- - Festus Keyamo

The Cable tace Lauyan ya nuna idan aka duba da kyau, za a ga haraji aka cire daga asusun, babu abin da ya hada akawun din da harkar kwayoyi.

Kana samun hutu? - IBB ga Tinubu

A makon nan aka ji labari Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya karbi bakuncin ‘Dan takaran APC, Bola Ahmed Tinubu da ‘yan tawagarsa a gidansa.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

Tinubu ya shaidawa tsohon shugaban na soja cewa ya kan huta domin ya ba jikinsa lafiya, yayin da tsohon sojan ya yi masa tambaya a game da hakan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng