Yadda Jam’iyyar APC Ta Rasa Sanatoci 3 Masu-Ci a Muhimiyyar Jiha a Watanni 6
Kafin a shirya zaben fitar da gwani na shiga takarar 2023, duka Sanatocin Bauchi ‘Yan Jam’iyyar APC ne
Yanzu kuwa jam’iyya mai mulkin ba ta da Sanata ko daya daga cikin ‘Yan majalisar dattawan yankin Bauchi
Sanata Halliru Dauda Jika, Lawal Yahaya Gumau da Muhammad Adamu Bulkachuwa sun sauya-sheka
A wannan rahoto, Legit.ng Hausa za ta kawo maku yadda siyasar Bauchi ta canza, APC tayi barin Sanatocinta uku daga watan Yuni zuwa yanzu.
Biyu daga cikin Sanatocin Bauchi sun tsallaka zuwa jam’iyyar hamayya ta NNPP mai kayan marmari, yayin da dayan ya sauya-sheka zuwa PDP.
Halliru Dauda Jika shi ne zai yi wa NNPP takarar Gwamna a 2023, yayin da Lawal Yahaya Gumau zai jarraba sa’a wajen neman kujerar da yake kai.
Sanatocin Bauchi da suka bar APC
1. Halliru Dauda Jika
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Halliru Dauda Jika bai nemi tikitin tazarce a zaben 2023 ba, ya nemi zama ‘dan takarar Gwamna ne amma ya sha kashi a hannun Sadiq Baba Abubakar.
Uba Ahmad Nana ne zai yi wa jam’iyyar takarar Sanata a zabe mai zuwa, yayin da Sanata Jika ya koma NNPP, har kuma ya samu takarar kujerar Gwamna.
2. Lawal Yahaya Gumau
A zaben tsaida gwani na APC na Kudancin Bauci, Sanata mai-ci Lawal Yahaya Gumau ya tashi da kuri’u 182, Shehu Buba Umar kuwa ya yi nasara da 188.
Rasa takaran ya jawo Sanata Gumau ya shiga jam’iyyar NNPP, kuma ya yi galaba a kan Shehu Abdullahi da Musa Maijama’a wajen samun tikitin tazarce.
3. Muhammad Adamu Bulkachuwa
A zaben tsaida gwanin da APC tayi, Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa na Arewacin Bauchi bai samu ko kuri’a guda ba, Siraj Tanko ne ya doke shi.
A makon nan sai aka ji Muhammad Bulkachuwa ya sauya-sheka daga APC. Duk da ya makara wajen samun takara, Sanatan ya shiga jam’iyyar adawa ta PDP.
Mutuwar yawa a Bauchi
A watannin baya an samu rahoto cewa Sanata Muhammad Adamu Bulkachuwa ya yi mummunar faduwa a zaben fitar da gwani na APC a jihar Bauchi.
Haka zalika Halliru Dauda Jika da Lawal Yahaya Gumau ba za su yi wa APC takara a 2023 ba, bayan sun sha kashi wajen neman tuta a jam'iyya mai mulki.
Asali: Legit.ng