Tinubu Ba Zai Wawure Dukiyar Jama’a Ba Idan Aka Zabe Shi Ya Gaji Buhari, Inji Jigon APC

Tinubu Ba Zai Wawure Dukiyar Jama’a Ba Idan Aka Zabe Shi Ya Gaji Buhari, Inji Jigon APC

  • An siffanta Bola Ahmad Tinubu da matsayin wanda bai da sha'awar sace kudin kasar nan idan aka zabe shi ya zama shugaban kasa a 2023
  • Wani jigon jam'iyyar APC dan jihar Zamfara ya bayyana cewa, Tinubu na da kudi da dukiyar da ba za ta bari ya saci na kasa ba
  • Yusuf Idris ya kuma bayyana cewa, abin da Tinubu ya sa a gaba shi ne yadda zai ci gaba daga inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya

Zamfara - A shirin zaben 2023 mai zuwa, an siffanta Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa a APC a matsayin mutum mai arziki kuma wanda zai mai da hankali ga tattalina arzikin Najeriya.

Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Zamfara ne ya bayyana hakan game da Tinubu, inda ya ce yana da yakinin Tinubu zai mayar da hankali ga ci gaban tattalin arziki da batun inganta tsaro.ity in the country.

Kara karanta wannan

Ku yi hakuri: Gwamnan da ya muzanta Fulani ya kira su 'yan ta'adda ya nemi gafararsu

Jaridar Vanguard ruwaito Yusuf Idris, kakakin APC a Zamfara na cewa, 'yan Najeriya su daure su ba da kuri'unsu ga Tinubu domin ganin sauyi na gaske game da ci gaban kasar nan.

Tinubu ba barawo bane, ba zai saci kudin Najeriya ba, inji jigon APC
Tinubu Ba Zai Wawure Dukiyar Jama’a Ba Idan Aka Zabe Shi Ya Gaji Buhari, Inji Jigon APC | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Idris ya kuma tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, Tinubu zai saka murmushi a fuskokinsu idan har ya kashe zaben 2023 mai zuwa nan kusa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu dan kasuwa ne, zai iya habaka tattalin arzikin kasa, inji Idris

Da yake karin haske, Idris ya ce, Tinubu sanannen dan kasuwa ne, kuma zai ba da himma sosai wajen habaka tattalin arzikin kasar nan.

A cewarsa:

"Shi (Tinubu) yana da gogewa sosai a fannin tattalin arziki, tsari da shugabanci. Yana da kwarewar ci gaba da ayyukan shugaban kasa Muhammadu Buhari har ma ya dara shi.
"Tabbas zai dara shi (Buhari) saboda kowane uba na gari zai so dan sa ya gaje shi kuma Tinubu zai zama magajin Buhari na gari."

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

Ya kuma bayyana cewa, Tinubu mai matukar imani da tsarin dimokradiyya ne, inda ya siffanta shi da shugaban da zai yi aiki kamar na soja amma ya tafiyar da jama'a kan turbar dimokradiyya, People Gazette ta tattaro.

A karin bayanin da ya yi, Idris ya ce Tinubu ba mai gwadayi bane, kuma bai da rowa, don haka ba zai saci kudin al'umma ba.

APC na samun tsaiko, sanata ya sauya sheka

Sai dai, duk da haka jam'iyyar APC na samun tsaiko ganin yadda wasu jiga-jigai ke sauya sheka gabanin zaben na 2023.

A yau ne muka samu labarin wani sanatan APC da ya saiya sheka PDP, ya bi sahun tafiyar Atiku Abubakar.

Dukkan jam'iyyun siyasa na fuskantar irin wadannan matsaloli da sauya sheka yayin da ake ci gaba da tunkarar zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.