Wasu Sun Je Kotu Domin Hana Tinubu Shiga Zabe, Alkali Ya Fara Biya Masu Bukata
- Babban kotun tarayya da ke Abuja yana sauraron karar da aka shigar a kan takarar Asiwaju Bola Tinubu
- Incorporated Trustees of Kingdom Human Rights Foundation International na so a hana Bola Tinubu shiga zabe
- Alkali yace dole APC, Bola Tinubu da Hukumar INEC su zo gaban kotun na Abuja domin su kare kansu a shari’a
Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja, ta umarci hukumar INEC ta duba sabon karar da aka shigar a kan takarar Asiwaju Bola Tinubu.
Vanguard tace an shigar da kara a gaban kotu domin a hana ‘dan takaran APC, Bola Tinubu shiga zaben shugaban kasa a bisa zargin sabawa dokar zabe.
Lauyan da ya shigar da wannan kara, Jideobi Johnmary yana rokon kotu ta cire sunan Bola Ahmed Tinubu a sahun masu neman zama shugaban kasa.
An rahoto cewa Johnmary yana zargin hukumar INEC ta ki amfani da karfin da ta ke da shi a doka wajen hana Tinubu shiga takara duk da ya saba doka.
Rokon da Lauya yake yi a kotu
Abin da lauyan yake so shi ne Alkali yace ‘dan takaran na jam’iyyar APC mai mulki bai cikin wadanda za su nemi kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sannan wanda ya shigar da karar yana so hukumar INEC tayi amfani da ikon da sashe na 84 (13) na dokar zabe ya bata, domin fatali da takarar Tinubu.
Jaridar Sun tace daga cikin rokon da Jideobi Johnmary yake yi shi ne kotu tace an saba ka’ida da doka wajen ba tsohon gwamnan na Legas takara.
Masu karar sun ce wannan shari’a za ta taimaka wajen tabbatar da gaskiya da kuma gyara damukaradiyyar Najeriya tare da bin doka wajen bada tikiti.
Hukuncin da aka fara yi
Mai shari’a Ahmed Mohammed ya saurari wannan kara da yake gabansa, ya kuma umarci a tursasa shugaban INEC, Mahmood Yakubu ya kare hukumarsa.
Rahoton yace Alkalin ya amince kungiyar 'Incorporated Trustees of Kingdom Human Rights Foundation Intl' ta tursasa Farfesa Mahmood Yakubu.
Da yake sauraron karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1960/2022, Alkali yace dole duka wadanda ake tuhuma su kare kansu kafin ranar 15 ga watan Nuwamba.
APC da rikicin kotu
Kwanakin baya an samu rahoto cewa APC ta damu da hukuncin da kotu tayi na ruguza tsaida Isiaka Oyetola a matsayin ‘dan takarar Gwamnan Osun.
Idan kotu ta tabbatar da bata ayyukan da Mai Mala Buni ya yi a jam'iyya mai mulki, za a iya rusa majalisar gudanarwa na NWC da lissafin ‘yan takaran 2023.
Asali: Legit.ng