Gwamnonin G5 Sun Yi Wa Ayu Izgili A Yayin Da Ortom Ya Nada Wa Hanyar Zuwa Gidan Shugaban PDP Sunan Wike
- Gwamnoni 5 da ke neman a cire ciyaman na PDP na kasa, Iyorchia Ayu, a ranar Litinin sun taru a Makurdi, babban birnin jihar Benue, don taya daya cikinsu, Samuel Ortom, murna
- Ortom ya fara wasu ayyuka a jiharsa kuma ya kammala su, hakan yasa gwamnonin 5 suka taho domin kaddamar da su
- Daya daga cikin ayyukan shine titi mai tsawon kilomita 2.1 da ya mike zuwa gidan Ayu da aka nada wa sunan Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da ke kiran a cire Ayu
Benue, Makurdi - Gwamnoni biyar da ke fushi da jam'iyyar PDP da aka fi sani da G5, a jiya sun kafa tarihi a Makurdi, babban birnin jihar Benue, a yayin da suka hallarci kaddamar da ayyukan da Samuel Ortom ya fara ya kuma kammala.
A cewar Channels Television, Ortom ya karbi bakuncin Seyi Makinde na jihar Oyo, Nyesom Wike na jihar Ribas, Okezie Ikpeazu na Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abin da ake ciki yanzu a PDP
Gwamnonin sun jadada bukatunsu, sau da dama suna neman a cire shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu.
A ranar Litinin, 7 ga watan Nuwamba, Gwamna Ortom ya nada wa titi mai nisan kilomita 2.1 da ya gina, sunan Nyesom Wike.
Titin na bayan rukunin gidajen kwamishinoni a babban birnin jihar kuma hanyar ce ta mike zuwa gidan Ayu. Tsohon gwamnan jihar Gabriel Suswam ya kaddamar da titin, Vanguard ta rahoto.
Nyesom Wike, Iyorchia Ayu, Samuel Ortom na PDP da zaben 2023
Gwamnonin na G5 da suka yi magana tunda farko sun yi kira ga magoya bayan su a jihar su zabi yan takarar PDP a jihar Benue.
Dan takarar gwamna na PDP a jihar shine kakakin majalisar dokokin jihar, Titus Uba.
Abin Da Wike Ya Fada Wa Atiku A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi Kan Rikicin PDP
A kokarin sulhu kan rikicin jam'iyyar PDP, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alh. Atiku Abubakar ya sake ganawa da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas.
Wata majiya da ta halarci taron ta shaidawa Daily Trust cewa wasu hadiminan bangarorin biyu sun halarci taron.
A ranar Alhamis a gidan gwamnatin Robas da ke Asokoro Abuja aka yi ganawar.
Asali: Legit.ng