Dan Takarar Majalisar Wakilai ta Kasa a Jihar Enugu Ya Rasu a Hadarin Mota
- Wani labari mara dadi da muke samu ya bayyana yadda wan dan takarar majalisar wakilai ya rasu a hadarin mota
- Pharm. Ejikeme Omeje, jigo a APC ya rasu ne yayin da yake dawowa daga wani taron siyasa da aka gudanar
- Jiga-jigan siyasa da dama ne suka rasu a 'yan kwanakin nan, ciki har da shugaban PDP na jihar Zamfara
Jihar Enugu - Dan takarar majalisar wakilai ta kasa daga mazabar Nsukka/Igbo-Eze ta Kudu a jam'iyyar APC, Pharm. Ejikeme Omeje ya riga mu gidan gaskiya.
Omeje, wanda daya ne daga jiga-jigan APC a jihar Enugu ya rasu ne a wani hadarin mota a yau Talata 8 ga watan Nuwamba da safe.
Hadarin ya auku ne a kan titin Edun Ani/Nsukka, daura da otal na El-Rina da ke Nsukka.
Rahotanni sun bayyana cewa, hadarin ya rutsa dashi ne yayin da yake dawowa daga wata tattaunar siyasa da aka yi a garin Edem-Ani, New Telegraph ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda lamarin ya faru
An ce kuma yana tuki ne a hanyar Erina-Edem Ani yayin da motar ta kubce masa ya dumfari daji, ya daki itace a garin neman tsira.
An gaggauta daukarsa zuwa asibiti domin jinyar ciwon da ya ji lokacin hadarin, amma rai ya yi halinsa.
Wani jigon APC ne ya tabbatar rasuwarsa ga majiya.
Wani shaidan gani da ido, Okechukwu Ezeme da ya zanta da wakilin jaridar Punch an garzaya da Omeje zuwa asibiti, amma ya rasu saboda raunukan da ya samu a kansa.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba samu jin ta bakin mai maganda yawun rundunar 'yan sandan jihar ba, Daniel Ndukwe.
Allah ya yiwa shugaban PDP a Zamfara rasuwa
A wani rahoton kuma, shugaban PDP na jihar Zamfara, Ahmad Sani ya riga mu gidan gaskiya, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.
Ya yanki jiki ne ya fadi yayin da ake tsaka da taron zaman lafiya kan zaben 2023 mai zuwa a birnin Gusau na jihar.
Rasuwarsa na zuwa ne watanni kasa da biyu da zabarsa a matsayin shugaban jam'iyyar, inda zai shafe shekaru uku a kujerar, kamar yadda ka'idar jam'iyya ta tanada.
Asali: Legit.ng