Tinubu, Atiku Sun Gagara Halartar Taron ‘Yan Takara, Kwankwaso, Obi Sun Yi Kasuwa

Tinubu, Atiku Sun Gagara Halartar Taron ‘Yan Takara, Kwankwaso, Obi Sun Yi Kasuwa

  • Asiwaju Bola Tinubu bai cikin wadanda suka halarci zaman da aka yi da masu neman mulkin Najeriya
  • Shi ma ‘Dan takaran PDP, Atiku Abubakar yana kasar waje don haka sai dai ya tura Dr. Ifeanyi Okowa
  • Rabiu Musa Kwankwaso, Peter Obi da Kola Abiola sun yi jawabi game da batun tattalin arziki da tsaro

Abuja - Biyu daga cikin manyan masu neman mukamin shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu da Atiku Abubakar ba su halarci taron ‘yan takara ba.

Premium Times ta kawo rahoto a daren Litinin, 6 ga watan Nuwamba 2022 cewa Gwamna Ifeanyi Okowa ya samu wakiltar Atiku Abubakar na PDP.

A gefe guda, Bola Tinubu bai samu zuwa ba, kuma bai aiko da wani wakili zuwa wajen taron da cibiyar CDD da gidan talabajin Arise suka shirya ba.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Gwamnan PDP da Ya Raba Jiha da Atiku Zai Yi wa Tinubu Aiki a Zaben 2023

Sauran ‘yan takaran da aka gayyata irinsu Peter Obi na jam’iyyar LP da kuma ‘dan takaran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso sun amsa goron gayatta.

Yadda aka zakulo 'yan takara

Cibiyar CDD ta gudanar da zabe inda a karshe aka gayyaci jami’iyyun da suka fi samun kuri’u da su turo ‘dan takaransu domin ya tattauna da al’umma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jam’iyyun siyasar da suka fi yawan kuri’u a zaben su ne – LP, APC, PDP da NNPP.

LP - 96.6%, APC - 86.2%, PDP - 82.8%, sai kuma jam’iyyar NNPP mai 51.7%.

'Yan takara
Taron 'Yan takaran Shugaban kasa Hoto: @MB_Shehu_Fagge
Asali: Twitter

Rahoton yace Reuben Abati ya bada uzurin Atiku Abubakar wanda aka ce yana hanyar dawowa daga kasar Morocco, don haka ya turo abokin takararsa.

Taro ya nemi jawo surutu

Legit.ng.Hausa ta fahimci wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun nemi a hana Okowa tsayawa a madadin Atiku, domin ba shi ne yake takara ba.

Kara karanta wannan

APC Tayi wa Gwamna Tsirara a Dangi, Ta Karbe ‘Yanuwansa daga Jam’iyyar PDP

Abin mamakin shi ne an gayyaci Kola Abiola na PRP, duk da jam’iyyarsa ba ta cikin sahun farko. APC ba ta kawo uzurin rashin aiko da 'dan takaranta ba.

The Cable tace a zaman farkon da aka yi na Lahadi, an tattauna da ‘yan takaran ne a kan abubuwan da suka shafi sha’anin tsaro da kuma tattalin arzikin kasa.

Da ya tashi yin na shi jawabin, shi ma Rabiu Kwankwaso wanda ya rike Ministan tsaro a gwamnatin Olusegun Obasanjo, ya gabatar da manufofinsa.

Peter Obi ya yi bayanin yadda zai magance matsaloli da yadda ya yi a lokacin yana gwamna. Har yanzu labarin wannan taro ake yi a dandalin Twitter.

Okezie Ikpeazu zai bi APC?

Ba boyayyen abu bane cewa babu jituwa tsakanin Atiku Abubakar mai neman takarar shugabancin Najeriya a 2023 da wasu Gwamnonin jihohin PDP.

An samu rahoto cewa John Okiyi Kalu yace duk abin da zai je ya dawo a jam’iyyar PDP, Gwamna Okezie Ikpeazu ba zai taba taimakon Bola Tinubu a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Jigo Ya Gargadi Jam’iyya, Yace ‘Dan Takaran Kano Yana Tare da Atiku

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng