Gwamnan PDP yace a Rabu da Jam’iyya, Ya Ajiye Atiku a Gefe, Yana Tallata Peter Obi

Gwamnan PDP yace a Rabu da Jam’iyya, Ya Ajiye Atiku a Gefe, Yana Tallata Peter Obi

  • Samuel Ortom ya yabi Peter Obi a lokacin da ‘dan takaran ya kai masa ziyara har garin Benuwai
  • Gwamnan na jihar Benuwai yace Obi ne ya fi cancanta yayi mulki domin zai iya gyara Najeriya
  • Amma saboda shi ‘dan Jam’iyyar PDP ne, Ortom yace ba zai iya taimakawa Obi ba, illa da addu’o’i

Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai yace Peter Obi mai neman shugabanci a inuwar jam’iyyar LP, shi ne wanda ya fi cancanta.

Vanguard tace Mai girma Samuel Ortom ya bayyana haka lokacin da Peter Obi ya kai masa ziyara a babban birnin jihar Benuwai watau garin Benuwai.

‘Dan takarar kujerar shugabancin kasar na 2023 ya je garin Makurdi domin ya gana da mutanen da annobar ambaliya ta auka masu a kwanakin baya.

A nan aka ji Gwamna Ortom yana yabon Obi, yace yana cikin ‘yan takaran da suka fi kyau.

Gwamnan mai barin gado a Mayun 2023 yace ‘dan takaran na LP zai iya shawo kan matsalar tattalin arziki da kuma rashin tsaro da ake fama da su.

“Idan Najeriya za tayi zabi, kana cikin ‘yan takara mafi kyawu da muke da su a kasar nan. A bangaren ilmi, halayya, aiki a ofis da neman mutane.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan PDP
Peter Obi da Samuel Ortom Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter
A wajen kishin kasa, kokarin samar da sana’o’i domin ganin kasar mu ta fita daga halin da ake ciki na rashin tsaro zuwa ga matsin tattalin arziki da rashin walwalar rayuwa, za ka iya kawo gyara.

- Gwamna Samuel Ortom

A rabu da kabilanci ko jam'iyya

Jaridar tace Gwamnan Benuwan yace bai kamata ayi la’akari da kabilanci ko jam’iyya wajen zaben shugaban da zai gyara matsalolin Najeriya ba.

A jawabinsa, Ortom ya nuna ko da mutum bai da kafuwa a siyasa, idan Ubangiji ya nufa zai yi shugabanci, zai iya doke duk wani ‘dan takara a filin zabe.

Amma ba zan iya yi maka komai ba

Baya ga kokarin da yayi a lokacin da yake rike da mukami, Gwamnan jam’iyyar ta PDP yace tsohon gwamnan jihar Anambran zai iya gyara kasar nan.

Duk da ya yabi ‘dan takaran, Ortom yace babu abin da zai iya yi wa Obi a 2023 domin shi ‘dan jam’iyyar PDP ne don haka sai dai kawai ya yi wa LP addu’a.

Kuri'u 5m daga Legas

Dazu an samu rahoto Bola Ahmed Tinubu yana so ya bar wa Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da sauran ‘Yan takara ragowar kuri’u miliyun biyu a Legas

Ganin daga Legas ‘Dan takaran na APC ya fito - jihar da ta fi kowace yawan PVC, Tinubu yana hangen 70% na kuri’un mutanensa a zaben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel