Zan Sayar da Matatun Mai Ga ’Yan Kasuwa Idan Na Gaji Buhari, Inji Atiku
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya sake jaddada aniyarsa ta siyar da matatun man kasar nan idan ya zama shugaban kasa
- Atiki Abubakar ya bayyana kwarin gwiwarsa a kan 'yan kasuwa, ya ce su ne za su iya rike matatun mai
- Ba wannan ne karon farko da ya yi wannan batu ba, a 2019 ya taba bayyana manufarsa mai kama da wannan
Washington DC, Amurka - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana manufarsa ta siyar da matatun mai Najeriya ga 'yan kasuwa idan aka zabe a 2023.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da gidan rediyon Amurka (VOA Hausa) a ziyarar da ya kai birnin Washington DC ta kasar Amurka.
Ya bayyana cewa, matsayarsa game da batun siyar da matatun mai ba sabon lamari bane, domin a cewarsa ya sha fadin inda ya dosa, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma bayyana cewa, ba 'yan kasuwa ragamar tafiyar da matatun zai fi haifar da mai ido ga Najeriya, don haka yake fatan zama shugaban kasa don ya cimma hakan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya maganar sace danyen mai da ake a Najeriya?
Da yake tsokaci game da satar man fetur a yankin Kudancin Najeriya, tsohon mataimakin shugaban kasan ya yi alkawarin samar da mafita mai dorewa idan ya zama shugaban kasa.
A cewarsa:
"Wannan wata matsala ce ta daban wacce za mu duba yadda za mu shawo kanta ta hanyar amfani da karfin ikon gwamnati, saboda dole a samu hadin kai tsakanin NNPC da sauran hukumomin tsaron da ke da alhakin kula da bututun mai da ake dashi."
A shekarar 2019, Atiku Abubakar ya taba bayyana muradinsa na siyar da matatun man fetur ga 'yan kasuwa, lamarin da ya jawo masa matsala gabanin zabe, rahoton Ripples Nigeria.
Najeriya dai na da matatun mai a Kaduna, Warri da Fatakwal sai dai ba sa aiki yadda ya kamata, wannan yasa ake shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje.
Majalisar Dattawa Za Ta Titsiye Ministar Kudi Kan N147bn Na Wutar Lantarki
A wani labarin, kwamitin majalisar dattawa kan makamashi ya gayyaci ministan kudi, Zainab Ahmed kan wasu kudade N147bn na ayyukan da aka nufi yi a ma'aikatar makamashi ta Najeriya.
Shugaban kwamitin, sanata Gabriel Suswan ne ya bayyana gayyatar ministar a yayin da ma'aikatar makamashi ke kare kasafin kudi a gaban kwamitin, Punch ta ruwaito.
Kwamitin na Suswan ya bayyana damuwa game da manufar kashe kudin a wasu ayyuka, wanda aka gaza ba da bahasi a kai.
Asali: Legit.ng