Gwamnan PDP Ya Soki CBN, Ya Fadi Dalilin Canza N200, N500 da N1000 Daf da Zabe

Gwamnan PDP Ya Soki CBN, Ya Fadi Dalilin Canza N200, N500 da N1000 Daf da Zabe

  • Gwamnan Edo yana adawa da canjin kudi da gwamnan babban bankin Najeriya na CBN yace za ayi
  • Godwin Obaseki yana zargin an kawo wannan manufa ne da nufin APC ta samu nasara a zaben 2023
  • Ganin halin tattalin arzikin da ake ciki, Obaseki yace ba buga sababbin kudi ne matsalar kasar nan ba

Edo - Mai girma gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya soki manufar babban bankin Najeriya watau CBN na buga sababbin takardun kudi.

A rahoton da muka samu daga The Cable, Gwamna Godwin Obaseki yace gwamnatin APC ta zo da wannan dabara ne domin samu kuri’u a 2023.

Godwin Obaseki yake cewa bai kamata a maida hankali wajen buga wasu takardun kudi ba, alhali mafi yawan mutane na cikin yunwa da talauci.

Kara karanta wannan

Bayan Abuja, Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

Obaseki yana ganin cewa abin da ya dace shi ne a magance matsin lambar tattalin arziki da ake fama da shi, ba a shiga fito da sababbin Naira ba.

Gwamnan ya yi wannan bayani ne wajen rantsar da kwamitin mata na yakin neman zaben jam’iyyar PDP da aka yi ranar Laraba a birnin Benin.

Gwamnan Edo
Gwamna Godwin Obaseki Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Sun ce mu fito da duka Nairorinmu, mu ba su domin su canza mana. Wannan shi ne abin da ya fi ci mana tuwo a kwarya a halin yanzu?
Canza Naira zai jawo farashin abinci a kasuwa ya ragu? Sun ce za su canza kudinmu, amma kullum Dala na tashi, an ma daina ganinta.
A matsayin masanin tattalin arziki, zan iya fada maku cewa wannan tsari na CBN da gwamnatin tarayya bai da madogara ta fuskar tattali.

Kara karanta wannan

Sabbin N500 tun na 2007: An fara ciro tsohuwar ajiya, kudin 2007 ya fara yawo a Najeriya

Babu dalilin wannan, tsan-tsagwaron siyasa ce, babu dalilin gaggawar canza kudinmu.”

- Godwin Obaseki

Canjin kudi a lokacin zabe?

Daily Trust tace Obaseki yace idan aka duba saura kwanaki 30 ayi zabe aka dauko wannan tsari, za a fahimci an yi hakan ne saboda manufar siyasa.

An ji Obaseki yana kira ga gwamnati ta kawo tsarin da za sai saukake samun kudin waje domin Najeriya ta dogara ne da shigo da kaya daga ketare.

Ina tare da CBN - Moghalu

A karshen makon da ya gabata, labari ya zo cewa Kingsley Moghalu ya yabi Gwamnan bankin CBN a kan maganar sake buga takardun kudi.

Tsohon mataimakin gwamnan na CBN yace akwai bukatar a canza kudin idan aka duba lamarin tsaro, amma yace hakan ba zai hana tashin farashi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel