Ana Tsaka Rikici, Jam'iyyar PDP Ta Kasa Ta Nada Sabon Shugaba a Katsina
- Jam'iyyar PDP ta amince da naɗin Alhaji Salisu Lawal-Uli a matsayin shugaban reshenta na jihar Katsina
- Wannan na zuwa ne yayin da sabon rikici ya ɓalle tsakanin ɗan takarar gwamna, Yakubu Lado da tsohon shugaba, Alhaji Majigiri
- Wasu bayanai sun nuna cewa Lado ya haɗa wata tawaga domin tsige Majigiri, wanda tuni ya sauka daga mukamin
Katsina - Kwamitin zartaswa (NEC) na jam'iyyar PDP ta ƙasa ya naɗa Alhaji Salisu Lawal-Uli, a matsayin sabon muƙaddashin shugaban jam'iyyar reshen jihar Katsina.
Wannan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP (NWC) ya rubuta mai ɗauke da kwanan watan 26 ga watan Oktoba, 2022 kuma Sakataren tsare-tsare, Alhaji Umar Bature, ya rattaɓa hannu.
Sabon shugaban PDP da aka naɗa, Alhaji Salisu Lawal-Uli ne ya raba kwafin takardar ga manema labarai ranar Laraba a Katsina, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Wasiƙar tace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Sakamkon zaɓen shugaban PDP na Katsina, Alhaji Salisu Majigiri a matsayin ɗan takarar majalisar wakilan tarayya, NWC a madadin NEC ta amince da naɗinka a matsayin muƙaddashin shugaba na jihar."
"Yayin da muke taya ka murnar sabon mukamin da aka baka, Ina mai amfani da wannan damar wajen jan hankalinka da ka tafiyar da jagoranci kan Demokaraɗiyya kamar yadda yake ƙunshe a kundin dokokin jam'iyya."
"Muna fatan zaka aiko mana da takardar amsar wannan muƙamin kuma muna maka fatan alheri a zangon mulkinka."
A cewar wasikar, Alhaji Lawal Uli, zai yi aiki ne a matsayin shugaban PDP na riko. Majigiri ya rike shugabancin PDP a Katsina tsawon shekaru 7 yayin da Lawal Uli ke matsayin mataimakinsa.
Tun da farko dai, Majigiri ya yi murabus daga mukamin domin neman tikitin takarar gwamna amma ya yi rashin nasara a hannun Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke, The Nation ta ruwaito.
Legit.ng Hausa ta gano cewa a halin yanzu Alhaji Majigiri ne ɗan takarar mamban majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Matsi/Dutsi karkashin inuwar PDP a zabe mai zuwa.
Kotu Ta Soke Zaɓen Fidda gwanin PDP a Kaduna ta tsakiya
A wani labarin kuma Babbar Kotu Ta Rushe Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar PDP na Mazaɓar Sanatan Kaduna ta tsakiya
Alkalin Kotun dake zama a Kaduna, Mai Shari'a Muhammad Umar, ya umarci jam'iyyar ta sake sabon zabe nan da mako biyu.
Daya daga cikin yan takara, Ibrahim Usman ne ya kai ƙarar, inda ya shaida wa Kotu cewa an yi aringizon ƙuri'u.
Asali: Legit.ng